Tag: Ƙidaya
-
Ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta gudanar da ƙidayar dabbobi
Farfesa Olajide Babayemi na sashen nazarin kimiyar dabbobi na tsangayar aikin gona ta jami’ar Ibadan ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta gudanar da ƙidayar jama’a domin tabbatar da adadin dabbobin da ke ƙasar nan. Mista Babayemi, wanda ya yi wannan ƙiran a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Legas ranar Laraba, ya…
-
Hukumar ƙidaya ta ƙasa, ta bayyana dalilin ɗage ranar ƙidaya a ƙasar
Hukumar ƙidaya ta ƙasa, (NPC), ta ce an ɗage ƙidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023 ne saboda shirin miƙa mulki na gwamnati da kuma yanayin da ƙasar ke ciki bayan zaɓe. Inuwa Jalingo, manajan ƙidaya na shekarar 2023 kuma darakta, hukumar ƙidaya ta ƙasa NPC, ya bayyana haka a wani taron manema labarai…
-
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗage ƙidayar jama’a
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ɗage shirin ƙidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023 da aka tsara. An bayyana ɗage ƙidayar ne bayan wata ganawa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da wasu membobin majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban hukumar ƙidaya ta ƙasa da tawagarsa a fadar shugaban ƙasa dake Abuja ranar Juma’a. Ku tuna…
-
Za a tsayar da ranar fara ƙidayar jama’a da gidaje a Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta ce za a fara aikin ƙidayar jama’a da gidaje na 2023 nan da watanni kaɗan dake tafe. Wani memba a kwamitin yaɗa labarai da bayar da shawarwari kan ƙidayar yawan jama’a da gidaje na ƙasa na shekarar 2023, Dakta Garba Abari, ya tabbatar da haka ranar Lahadi a Abuja. Ya ce aikin…
-
Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa ta shirya taron ƙarawa juna sani ga ‘Yan Jarida da ma’aikatanta
A ranar Alhamis, hukumar ƙidayar jama’a a Najeriya (NPC) ta shirya taron ƙarawa juna sani ga Ma’aikatanta da ‘yan jarida, domin samun ƙwarewa da kuma yaɗa yadda aikin ƙidayar zai kasance. Taron da hukumar ta NPC daga shiyyar jihar Katsina ta shiryashi na wuni ɗaya domin bita akan yadda aikin ƙidayar na zamani yake da…
-
Aikin ƙidayar 2023 zai lashe naira biliyan 400
Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, (NPC) ta ce an ware sama da Naira biliyan 400 domin ƙidayar jama’a ta shekarar 2023. Jick Lawrence, shugaban sashen hulɗa da jama’a na NPC a Filato, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke gabatar da maƙala a wajen wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya ga…
-
Hukumar Ƙidaya a Najeriya za ta ɗauki ma’aikatan wucin-gadi miliyan biyu – Kwamishina
Ayodeji Ajayi, kwamishinan tarayya mai wakiltar Ekiti a Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, (NPC), ya bayyana cewa za a ɗauki ma’aikatan wucin-gadi miliyan biyu da za su yi aikin ƙidaya. Ajayi ya bayyana hakan a Ado Ekiti a ranar Alhamis a wani taron manema labarai don sanar da jama’a game da shirin ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi domin…