Tag: Zabe
-
An tafka muhawarar farko tsakanin shugaba Biden da Trump
An tafka muhawarar farko tsakanin shugaba Biden da Trump Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban ƙasar Donald Trump sun gwabza muhawara a daren Alhamis, inda suka fafata kan tattalin arziƙin Amurka da harkokin ƙasashen waje da haƙƙin zubar da ciki da kuma batun ƙaura daga kan iyakar Mexico zuwa Amurka. “Muna tamkar a wata…
-
Ɗan takarar jam’iyyar adawa Bassirou na kan gaba a zaɓen Senegal
Sakamakon farko-farko da ke fitowa dangane da zaɓen Senegal na nuna cewa Bassirou Diomaye Faye ke kan gaba a zaɓen inda ake ganin zai iya samun ƙuri’u mafi rinjaye, sai dai abokin hamayyarsa da ke jam’iyya mai mulki ya ce akwai buƙatar a je zaɓe zagaye na biyu domin tantance wanda ya ci zaɓen. Tun…
-
Ƙasar Chadi ta sanar da ranar zaɓe don komawa tafarkin Dimokuraɗiyya
Hukumar zaɓen ƙasar Chadi ta ba da sanarwar ba zato a ranar Talata cewa, za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa wanda zai kawo ƙarshen mulkin soji na tsawon shekaru uku a yankin tsakiyar Afirka a ranar 6 ga watan Mayu. Hukumar zaɓe ta ƙasar Chadi ta ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa…
-
An hana gudanar da zanga-zanga a Senegal
Hukumomi a Senegal sun hana ƴan hamayya yin zanga-zanga ranar Talata a yayin da Amurka ta bi sahun masu ƙira ga Shugaba Macky Sall ya gudanar da zaɓe sannan ya sauƙa daga mulki. Mutum uku ne suka mutu tun lokacin da aka soma zanga-zanga a ƙasar bayan Shugaba Sall ya ɗage zaɓen da ya kamata…
-
INEC ta dakatar da wani jami’inta don gudanar da bincike kan ɓacewar takardun kaɗa ƙuri’a
Daga Maryam Umar Abdullahi Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta dakatar da wani jami’inta mai suna Mr Fred Ogboji, wanda ke kula da ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, bisa zargin ɓacewar wasu muhimman kayayyakin gudanar da zabe. Hukumar INEC, a wata sanarwa ta ce ta dakatar da jami’in nata ne don samun sukunin…
-
INEC ta cire PDP a jerin jami’iyyun da za su shiga zaɓe a Filato
Daga Maryam Umar Abdullahi Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta cire jami’iyyar PDP a jerin jami’iyyun da za su shiga zaɓen da za ta gudanar na ‘yan majalisun tarayya a shiyyar Arewacin jahar Filato. Gudanar da zaɓen ya biyo bayan shara’ar da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke, inda ta cire sanata mai…
-
An tsaurara tsaro a wajen ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a Adamawa
An tsaurara tsaro a lokacin da jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta na ƙasa (INEC) suka sake taro a cibiyar tattara sakamakon zaɓe a jihar Adamawa Jami’an tsaro sun isa cibiyar tattara sakamakon zaɓen jihar da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa yayin da jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ke ci…
-
Gwamnatin tarayya ta buƙaci ‘yan Najeriya da su sauke manhajar N-Alerts
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya buƙaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan manhaja ta N-Alerts smartphone domin kai rahoton matsalolin tsaro a lokacin zaɓen da za a fara gobe. Ministan ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan buƙata domin su kai rahoton duk wani yanayi…