Tag: Miliyan
-
EFCC ta ƙwato naira biliyan 60 a cikin kwana 100
Daga Ibraheem El-Tafseer Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta EFCC, a Najeriya, Mista Ola Olukoyede, ya ce a cikin kwana 100, ofishinsa ya samu ƙorafe-ƙorafe 5,000 da suka danganci almundahana, kuma ya samu ƙwato Naira biliyan 60. A cewar shugaban, hukumar ta samu ƙwato wasu $10m, a wannan tsawon lokacin,…
-
Ban kashe naira miliyan 400 wajen tafiya ƙasashen ƙetare ba – Lawal
Gwamnan jihar Zamfara dake Najeriya Dauda Lawal ya yi watsi da zargin da aka masa cewar ya hallaka kuɗin jiharsa da suka kai naira miliyan 400 wajen tafiye tafiye zuwa ƙasashen ƙetare. Wata jaridar da ake wallafawa a kafar intanet ta wallafa labarin, inda tace gwamnan ya kashe sama da naira miliyan 170 zuwa ƙasashen…
-
‘Yan Najeriya miliyan 2.6 na iya aukawa ƙangin yunwa a 2024
Hukumar samar da abinci da bunƙasa noma ta duniya ta ce ‘yan Najeriya aƙalla miliyan biyu da dubu 600, a jihohin Borno da Sokoto da Zamfara da kuma babban birnin ƙasar Abuja, na iya fuskantar matsalar rashin abinci a tsakanin watan Yuni da Agustan 2024. Wakilin hukumar, Dr. Abubakar Suleiman ne, ya bayyana haka yayin…
-
Bayan biyan miliyan biyar, ‘yan bindiga sun saki ɗaya daga cikin masu yiwa ƙasa hidima da aka yi garkuwa da su a Zamfara
Babban daraktan hukumar yiwa ƙasa hidima (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya ce an sako ɗaya daga cikin jami’an hukumar da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara a lokacin da suke tafiya daga garin Uyo na jihar Akwa Ibom zuwa jihar Sokoto tare da sauran bakwai da har yanzu ake hannunsu. Da yake…
-
Matuƙin Keke Napep ya mayar da miliyan 15 da wani fasinja ya manta a mashin ɗinsa
Wani matashi ɗan shekara 22 mai suna Auwalu Salisu ya mayar da Naira miliyan 15 da wani fasinja da ya zo daga ƙasar Chadi sayo kaya a Kano ya manta a mashin ɗinsa. Salisu ya mayar da kuɗin ne bayan an sanar da ɓacewarsu a wani gidan rediyo a Kano, PM News. Ya shaida wa…
-
Remi Tinubu ta ba da naira miliyan ɗari biyar ga ‘yan gudun hijira a Filato
Damuwa da tashe-tashen hankula a jihar Filato, a ranar Talata, uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta bayar da gudummawar naira miliyan 500 ga iyalai 500. Waɗanda suka ci gajiyar tallafin dai sun fito ne daga ƙananan hukumomi shida na jihar ta Arewa ta tsakiya. Sanata Tinubu ta je Jos babban birnin jihar ne domin jajanta…
-
Gwamnan Ribas ya ba da miliyan 100 ga wanda ya bayyana waɗanda suka kashe DPO a jihar
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ba da umarnin dakatar da wani sarki har sai baba ta gani dangane da kisan gillar da ‘yan iska suka yi wa jami’in ‘yan sanda na Ahoada, SP Baƙo Angbashim, da “gungun masu laifi.” A baya dai LIB ta ruwaito cewa an kashe Baƙo ne a yankin Odiemudie da…
-
‘Yan Najeriya miliyan 11 ne ke samun wutar lantarki – NBS
Adadin masu amfani da wutar lantarki ya ƙaru da 200,000 daga miliyan 11.27 a rubu’in farko na shekarar 2023 zuwa miliyan 11.47 a rubu na biyu na shekara. Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, (NBS), ta bayyana a cikin rahotonta na wutar lantarkin Najeriya na kashi na biyu na shekarar 2023 da aka fitar a Abuja ranar…
-
EFCC ta mayar wa wata mata miliyan 19 da gida da mota
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta miƙa kadarorin da ta ƙwato daga hannun wani ɗan damfara mai suna Aisosa Ohue, wanda aka fi sani da Frederick Leonard, ga wata Ba’amurke da aka kashe, Cheryldene Cook. Kakakin hukumar Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya…
-
NDLEA ta kama ɗan fashi da dala miliyan 20 na jabu
Hukumar NDLEA ta kama wani ɗan fashi mai suna Aliyu Altine mai shekaru 19 da ake nema ruwa a jallo a kan titin Illela zuwa Sakkwato a ranar Alhamis 17 ga watan Agusta. Hakazalika jami’an yaƙi da miyagun ƙwayoyi sun kama wasu jabun dala miliyan 20 a yayin gudanar da aikin “Tsaya-da-Bincike” a kan babbar…