Tag: Matawalle
-
‘Yan sanda sun mamaye gidan Matawalle, sun ƙwato motoci sama da 40
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan sandan Najeriya sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, domin ƙwato motoci da ake zargin tsohon gwamnan ya tafi da su. Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa a lokacin da aka kai samame gidan Matawalle a ranar Juma’a, an ce ‘yan sandan sun ƙwato Motoci guda huɗu…
-
Gwamnatin Zamfara ta bai wa Matawalle wa’adin mayar da motocin alfarma na biliyoyin nairori
Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta bai wa tsohon gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle wa’adin kwanaki biyar da ya bayar da bahasi kan motocin alfarma na biliyoyin nairori da aka sayo daga susun gwamnatin jihar, kuma suka yi ɓatan-dabo. A cikin wata sanarwa da babban mai taimaka wa gwamnan jihar kan…
-
Matawalle ya wawure motoci 17, injinan gas, da na’urorin talabijin na jami’an gwamnati – Gwamna Dauda
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya zargi tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, da yin awon gaba da motocin gwamnati guda 17, tare da wawure dukiyoyi da suka haɗa da na’urorin talabijin da injinan gas na masu dafa abinci a gidan gwamnatin jihar. Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa gwamna Lawal bayan rantsar da shi, ya…
-
Matawalle ya bar bashi mai tarin yawa a asusun jihar – Lawal Dare
Sabon gwamnan jihar Zamfara da aka rantsar, Dauda Lawal Dare, ya zargi tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, da barin asusun jihar da basussuka masu ɗimbin yawa. Lawal ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan an rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar a ranar Litinin. Gwamnan, ya yi alƙawarin kawo ci gaba cikin sauri tare…