Tag: Kamfani
-
Kamfanin wutar lantarki ta dawo da wuta a Sakkwato
Kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya dawo da wutar lantarki mai mai ƙarfi a jihar Sakkwato da karfe 6 na yammacin ranar Asabar 15 ga watan Satumba, kamar yadda wani jami’i ya tabbatar. Mista Ndidi Mbah, Babban Manaja na Hulɗa da Jama’a (GM) ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba…
-
Kamfanin dakon kaya ya gargaɗi maniyyata da su guji sayan abubuwan da aka haramta
Shugaban Kamfanin Sokodeke Cargo Travels and Tour Ltd., Ibrahim Mohammad, ya gargaɗi maniyyatan Najeriya da su guji saye da sanya haramtattun kayayyaki a cikin jakukkunan da aka amince da su. Mohammed ya yi wannan ƙiran ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da…
-
Motar kamfanin gine-gine ta kashe mutane 4, ta raunata 16 a jihar Kwara
Mutane 4 ne suka mutu yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Oloru zuwa sabuwar Jebba a ƙaramar hukumar Moro a jihar Kwara ranar Juma’a. Babban kwamandan hukumar FRSC a jihar Kwara, Frederick Ogidan, ya bayyana hakan a garin Ilorin ranar Lahadin da ta…
-
Hukumar NDLEA ta fasa kamfanin ‘Akuskura’ a Adamawa
Hukumar yaƙi da da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta ƙona wata masana’anta a Adamawa dake kai wa ƙasashen Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar sinadarin Akuskura. Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce an kai samame…
-
eNaira: CBN ya gayyaci wani kamfani na Amurka domin gyara lamarin– Rahoto
Domin samar da ingantaccen kuɗin dijital da kuma tabbatar da karɓuwar jama’a, Babban Bankin Najeriya ya tuntuɓi wani kamfanin fasaha na New York don saɓunta fasahar da ke cikinsa. A cewar rahoton Bloomberg, CBN na tattaunawa da sabbin ‘abokan fasaha’ don samar da wani sabon tsari da ingantaccen tsarin sarrafa eNaira. An ba da rahoton…
-
Sheraton Hotels ya koma Abuja Continental Hotel
Shaharren gidan saukar baki na Sheraton da ke Abuja daga yanzu za a rika kiransa da Abuja Continental Hotel,bayan da masu mallakina, Capital Hotels Plc, suka sanar da sauya sunan a takardar yarjejeniya da aka shigar. Bayanin ya nuna matakin farko na kamfani na Capital Hotels tun lokacin da kamfanin 22 Hospitality Limited ya samu…
-
Yadda yajin aikin ma’aikatan jiragen sama ya tayar da hayaniyar a filin jirgin saman Legas
Fasinjoji da dama na kasashen waje sun maƙale a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Litinin, yayin da aka tilastawa kamfanonin jiragen sama karkatar da zirga-zirgar jiragen sama, sakamakon yajin aikin da ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Nigerian Aviation Handling Company Plc (NAHCO) suka shiga, kan batutuwan…