Tag: Girgizar kasa
-
Girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.9 ta auka wa ƙasar Papua New Guinea
Mutum aƙalla biyar ne suka mutu, kana an ƙiyasta gidaje 1,000 da suka ruguje a lokacin da wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.9 ta auka wa arewacin Papua New Guinea, kamar yadda jami’ai suka bayyana, yayin da ma’aikatan takaita aukuwar bala’o’i ke ta ƙoƙarin kai ɗauki yankin. “Ya zuwa yanzu, an yi asarar kusan…
-
Girgizar ƙasa ta kashe sama da mutane 100 a arewa maso yammacin China
Aƙalla mutane 116 ne suka mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta ruguje gidaje a arewa maso yammacin ƙasar China, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ruwaito da safiyar Talatan nan, yayin da jami’an ceto suka dukufa wajen tona baraguzan gine-gine cikin wani yanayi mai sanyin gaske. Jami’ai a lardin Gansu da lamarin yafi…
-
Girgizar ƙasa mai karfin gaske ta kashe mutane 296 a Maroko
Sama da mutane 296 ne suka mutu sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfin awo 6.8 a Maroko, in ji jami’ai. Yawancin waɗanda suka mutun an ce sun kasance a yankunan da ke da wahalar isa a kudancin Marrakech. Girgizar ƙasar ta auku ne da sanyin safiyar Asabar – inda ta yi ɓarna a gine-gine a manyan…