Tag: cire
-
Da ba a cire tallafin mai ba, da wahalar da za’a sha a Najeriya ta fi ta yanzu – Gwamnatin tarayya
Daga Ibraheem El-Tafseer Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na Najeriya, Alhaji Mohammed Idris Malagi ya ce, da gwamnati ba ta cire tallafin mai ba da wahalar da ake ciki a ƙasar ta fi haka a yanzu. Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake kare matakin gwamnatin ƙasar na cire tallafin mai…
-
Kwamishinan ‘yan sanda ya cire DPO da yaransa kan zaluntar jama’a
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Idowu Owohunwa, ya bayar da umarnin korar jami’in ‘yan sandan DPO na ofishin ‘yan sanda na Meiran da ke jihar Lagos bisa zargin karɓar kuɗi. Tun da farko, wani Injiniya Ibrahim Saliu, wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai na PUNCH, ya yi iƙirarin cewa wasu ‘yan sandan da ke…
-
Shugaba Tinubu ya cire Abuja daga tsarin asusun ajiya na bai-ɗaya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya cire birnin tarayyar ƙasar Abuja daga tsarin Asusun Ajiya na Bai-ɗaya (TSA) Tinubu ya ɗauki matakin ne da nufin bayar da dama wajen bunƙasa ci gaban birnin ƙarƙashin jagorancin ministan Abuja Nyesom Wike, domin ba shi ƙarin iko kan kuɗaɗen da birnin ke tarawa. Ministan Abuja, Nyesom Wike ne…
-
Cire tallafin mai: COEASU ta umarci malamansu da su yi aikin kwanaki biyu a mako
Ƙungiyar malaman kwalejojin ilimi, (COEASU), ta umurci membobinta a faɗin ƙasar nan da su riƙa zuwa aiki kwana biyu a mako har sai gwamnatin tarayya ta biya buƙatar ta na ƙarin albashin kashi 200 cikin 100. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban COEASU na ƙasa, Dakta Smart…
-
Na zaɓi na cire tallafin man fetur a ranar farko duk da babu shi a jawabina – Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce shi da kansa ya zaɓi ya bayyana cire tallafin man fetur a ranar farko da ya zama shugaban ƙasa duk da cewa ba a rubuta shi ba a cikin jawabin da ya gabatar. Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da ‘yan Najeriya mazauna Faransa ranar…
-
Gwamnonin Najeriya sun goyi bayan cire tallafin man fetur
Gwamnonin jihohin Najeriya sun nuna goyon bayansu ga matakin da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na cire tallafin man fetur. Gwamnonin sun bayyana haka ne a lokacin wata ganawa da suka yi da shugaban ƙasar a yau Laraba. Wata sanarwa da ta fito ta hannun daraktan yaɗa labarai na fadar shugaban Najeriya, Abiodun…
-
A ƙarshe an cire tallafin man fetur, NNPC na sayar da man fetur 537 a Abuja
A ƙarshe Najeriya ta cire tallafin da take baiwa motoci ƙirar PMS wanda aka fi sani da Petrol a matsayin kamfanin mai na Nigeria National Petroleum Company (NNPC) Limited a safiyar Laraba a hukumance ta canza farashin famfunan man fetur zuwa Naira 537 ga kowace lita a Abuja, yayin da wasu yankunan suke da nasu…
-
El-Rufai, Soludo, Sanusi sun dage kan cire tallafin man fetur
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da takwaransa na Anambara, Charles Soludo, sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta kawo ƙarshen tsarin tallafin man fetur wanda ya yi illa ga tattalin arziƙin Najeriya. Gwamnonin sun yi wannan ƙiran ne a ranar Talata a Abuja yayin wani taron tattaunawa a kan manufofin “Yadda Najeriya za ta iya Gina…