Ta sace ‘yarta a Kano, ta nemi mijinta ya ba ta kuɗin fansa, miliyan uku

Wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Rahama Sulaiman, ta shiga hannun jami’an ‘yan sanda a Kano bisa zarginta da yin garkuwa da ‘yarta ‘yar shekara shida mai suna Hafsat Kabiru, tare da neman mijin ta a biya ta Naira miliyan uku, kuɗin fansa.

Matar dai ta kai yarinyar wurin wani ɗan uwanta dake unguwar Madobi domin ya ajiye mata kuma za ta yi tafiyar kwana huɗu.

Da yake magana a lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin da sauran masu laifin a hedikwatar ‘yan sandan Kano, kwamishinan ‘yan sandan, Muhammad Usaini Gumel, ya ce sun samu rahoto daga mijinta Kabiru Shehu, cewa an yi garkuwa da ‘yarsa.

KU KUMA KARANTA: Yadda yaro ɗan shekara 20 ya sace mahaifiyarsa, ya karɓi kuɗin fansa naira miliyan 30 a Zamfara

“A wani bincike da aka gudanar, an kuɓutar da wanda aka kama a ƙaramar hukumar Madobi kuma matar da mijin ya sake ta tun farko ta ce ta shirya sace ‘yarta.”

Da take zantawa da manema labarai bayan an kama ta, wadda ake zargin ta ce tsohon mijin nata bai ba ta kuɗin ciyar da yarinyar ba sama da watanni 10, don haka ta yanke shawarar yin hakan ne domin ta samu kuɗin kula da ‘ya’yansa.

“Na ƙira shi na ce masa ‘yarmu ta ɓace, muka je wurin ‘yan sanda tare muka kai rahoton lamarin. A cikin ofishin ‘yan sanda na ba shi lambar mutumin da zai karɓi kuɗin fansa,” inji ta.

Ta ce ta yi nadamar abin da ta aikata kuma ta sanar da cewa ta sasanta da mijinta. Mijin wanda ya tabbatar da cewa sun yi sulhu, ya ƙara da cewa matarsa ​​ba ta taɓa yin haka ba.

Rundunar ta kuma kama wasu masu laifin da suka haɗa da masu garkuwa da mutane da dillalan ƙwayoyi, sannan kuma sun ƙwato tabar wiwi sama da 600.

Sai dai CP ya ce za a gurfanar da duk waɗanda ake zargin bayan bincike.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *