Sojojin Najeriya sun ceto mutane huɗu, sun lalata sansanin ‘yan bindiga a Kaduna

0
276

Rundunar sojojin Najeriya ta ɗaya da ke Kaduna ta ce dakarunta sun ceto wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su tare da lalata sansanonin ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta 1 Division Nigerian Army, Lutanal Kanal Musa Yahaya, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Kaduna.

Yahaya ya ce an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ranar Litinin.

KU KUMA KARANTA: Sojoji a Zamfara sun kashe ‘yan bindiga bakwai, sun ƙwato alburusai da dama

“A ci gaba da gudanar da ayyukanta na ci gaba da yaƙi da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, ɓarayin gidan sarauta da sauran masu aikata laifuka a yankin Arewa maso Yamma.

“Dakarun runduna ta ɗaya ta Najeriya dake aiki da sahihan bayanan sirri sun kai wani samame a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Mista Yahaya ya bayyana cewa, a yayin farmakin, sojoji sun yi taho-mu-gama da ‘yan bindiga/ masu garkuwa da mutane, inda suka yi artabu da su.

Ya ce sun tunkare su da ƙarfin wuta wanda ya tilasta musu yin watsi da waɗanda suka yi garkuwa da su tare da kai musu ɗauki da raunuka daban-daban.

“Sojojin sun yi nasarar ceto hudu da aka yi garkuwa da su, sun kama babur ‘yan fashi tare da lalata sansaninsu,” in ji shi.

Mista Yayaha ya ce babban kwamandan runduna ta ɗaya ta Najeriya da kwamandan rundunar Operation Whirl Punch, Manjo janar Bamidele Alabi ya yabawa sojojin bisa jajircewa da ƙwarewa da suka nuna kafin aikin da kuma lokacin aikin.

Ya kuma buƙaci sojojin da su ci gaba da zage damtse domin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci na masu garkuwa da mutane da ɓarayin shanu da sauran laifuka a yankin da ke da alhakin gudanar da ayyukansu.

Ya kuma yi ƙira ga duk ‘yan ƙasa masu bin doka da oda da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na halal da kuma baiwa rundunar sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro damar samun bayanan sirri a kan lokaci.

Leave a Reply