No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sojojin Amurka za su kammala ficewa daga Nijar 15 ga Satumba

Sojojin Amurka da ke zaune a Nijar sun soma ficewa daga ƙasar kuma za su kammala ficewa daga ƙasar a ranar 15 ga watan Satumbar 2024, kamar yadda wata sanarwar haɗin-gwiwa ta bayyana wadda Amurka da Nijar ɗin suka fitar a ranar Lahadi.

Duka ɓangarorin biyu sun sanar da cewa sun cimma matsaya ta wareware dangantaka inda sojojin na Amurka suka soma ficewa bayan Nijar ɗin ta yi iƙirarin suna zaune ne ba bisa ƙa’ida ba.
Akwai sojojin Amurka kusan 1,100 a Nijar da ke zaune waɗanda Amurkar ta ce suna taimakawa domin yaƙi da ta’addanci.

A watan Maris, sojojin da ke mulki a Nijar suka bayyana cewa wata yarjejeniyar tsaro da aka cimmawa a 2012 tsakanin Nijar da Amurka an yi ta ne “ba tare da izinin” Nijar ba.

KU KUMA KARANTA: Rundunar sojin Najeriya ta nemi Nijar ta kama shugaban ‘yan bindiga da take nema

An kori sojojin Faransa

Nijar ta bayyana cewa Amurka ta yi ta ƙoƙarin hana ta dangantaka da Rasha, wadda tuni ta tura masu horar da sojoji da kayayyakin yaƙi domin su cike gurbin na Faransa waɗanda Nijar ɗin ta kora a kwanakin baya.

Nijar ɗin ta kori dakarun na Faransa 1,500 daga ƙasarta.

A watan Satumbar 2023, shugabannin sojin Nijar sun ce sojojin Faransa sun gaza yaki da ‘yan tada kayar baya duk da cewa sun shafe fiye da shekaru goma a ƙasar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...