Sojojin ƙasar Sudan sun bayyana aniyarsu ta komawa teburin shawara a Jeddah

0
330

Sojojin gwamnatin Sudan sun ce a ranar Alhamis mai zuwa za su koma teburin shawara tare da dakarun ko-ta-kwana na ƙasar ko RSF, a birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya.

Da yake ƙarin haske ga sojojin rundunar SAF kan hakan, a sansanin soji na Wadi Seidna dake birnin Omdurman, mataimakin kwamandan rundunar Shams-Eddin Kabashi, ya ce, “Mun samu gayyata zuwa tattaunawa a Jeddah, kuma tawagarmu za ta isa birnin na Jeddah domin fara shawarwari tun daga ranar Alhamis.”

Wata kafar watsa labarai ta Sudan ta rawaito cewa, masarautar Saudiyya da Amurka, waɗanda suke shiga tsakanin sassan biyu tun daga watan Mayu, su ne suka sake ayyana ranar komawa teburin tattaunawar.

Kafin hakan, an dakatar da zaman sulhu ne tun cikin watan Yuli, saboda wasu batutuwa manya, da suka haifar da saɓani tsakanin ɓangarorin sojin biyu na ƙasar Sudan.

KU KUMA KARANTA: Yankunan da ake tafka yaƙi a Sudan sun ƙara yawa

Dakarun SAF da na RSF sun fara ɗauki ba daɗi da juna ne a birnin Khartoum, da wasu ƙarin sassan ƙasar, tun daga ranar 15 ga watan Afirilun bana, wanda hakan ya haifar da kisan a ƙalla mutane 3,000, baya ga wasu sama da 6,000 da suka ji raunuka, kamar dai yadda ma’aikatar lafiyar ƙasar ta bayyana.

A ɗaya ɓangaren kuma, hukumar MDD mai lura da ’yan gudun hijira, ta ce kusan ’yan ƙasar ta Sudan miliyan 5.8 ne suka rasa matsugunan su a ciki da wajen ƙasa, sakamakon tsawaitar lokacin da aka kwashe ana gwabza faɗa tsakanin dakarun na SAF da RSF.

Leave a Reply