Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda shida, sun ƙwato makamai a Kaduna

2
507

Hedikwatar tsaro ta ce dakarun ‘Operation Forest Sanity’ tare da haɗin gwiwar hedkwatar tsaro na musamman sun kashe ‘yan ta’adda shida tare da ƙwato makamai da alburusai a jihar Kaduna.

Daraktan ayyukan yaɗa labarai na tsaro Musa Ɗanmadami ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Manjo Janar Ɗanmadami, ya ce a ranar Juma’ar da ta gabata ne sojojin suka gudanar da wani samame a ɓoye a yankunan ‘yan ta’adda a ƙauyen Maidaro da ke ƙaramar hukumar Giwa tare da tuntuɓar ‘yan ta’addan.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 58, sun kama 161

Ya ce an kawar da ‘yan ta’addan shida a yaƙin wuta da ya ɓarke. A cewarsa, an ƙwato bindigogin AK 47 guda biyar, alburusai mai tsayin 7.62 x 39 na musamman guda 192, alburusai 74 na musamman masu tsayin 7.62 x 54 da kuma na AK 47 guda tara.

“An ƙwato IED guda uku, rediyon Baofeng guda uku, PKM ɗaya, babura uku da sauran kayayyaki iri-iri.

“Babban kwamandan sojojin ya yaba wa sojoji tare da ƙarfafa gwiwar jama’a da su baiwa sojojin da sahihan bayanai masu inganci kan ‘yan ta’adda da duk wasu ayyukan aikata laifuka a yankinsu,” in ji shi.

2 COMMENTS

Leave a Reply