Siyasa ce ta sa aka cire min rawani na – Wazirin Gaya Murabus

0
166
Siyasa ce ta sa aka cire min rawani na - Wazirin Gaya Murabus
Alhaji Usman Alhaji, Wazirin Gaya da aka cire

Siyasa ce ta sa aka cire min rawani na – Wazirin Gaya Murabus

Daga Jameel Lawan Yakasai

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG), Alhaji Usman Alhaji, ya bayyana cire shi daga mukamin Wazirin Gaya da masarautar Gaya ta yi a matsayin abin da ba shi da tasiri kuma ya zo a makare.

A baya-bayan nan ne Alhaji Usman Alhaji ya zargi gwamnatin jihar da karɓar bashin ƙasashen waje na sama da dala miliyan $600 tare da ɓatar da kuɗin ba tare da bin ƙa’ida ba.

Kwana kaɗan bayan wannan zargi da ya yi, sai ga shi masarautar Gaya ta sanar da cire shi daga matsayin Wazirin Gaya.

KU KUMA KARANTA: Masarautar Gaya ta sauƙe Wazirin Gaya daga muƙaminsa

A martaninsa, Alhaji Usman Alhaji wanda shi ne ya kafa ƙungiyar APC Patriotic Volunteers, ya bayyana cewa wannan mataki na cire shi yana da nasaba da siyasa.

A cikin wata sanarwa da Dan’azumi Gwarzo ya sanyawa hannu a madadin ƙungiyar APC Patriotic Volunteers, Alhaji Usman Alhaji ya ce, cire mutum daga sarauta yana da hanyoyi da matakai da ya kamata a bi, wanda a cewarsa ba a bi ba a wannan lamari.

Ya ƙara da cewa rashin bin waɗannan matakai laifi ne kuma rashin adalci.

Sanarwar ta ce:
“Za ku iya tunawa cewa mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano sun kafa doka da ta soke dukkanin Sarakunan Farko da Masarautunsu a jihar. Saboda haka, Alhaji Usman Alhaji ya daina kasancewa Wazirin Masarautar Gaya.

“Na biyu, soke da rusa masarautun farko na Gaya, Rano, Karaye da Bichi ya biyo bayan kafa sabbin masarautu na matsayin sarakuna masu daraja ta biyu (wanda ya rage matsayin su daga na farko).

“Wannan ne dalilin da ya sa Wazirin Gaya Alhaji Usman Alhaji tare da wasu masu rike da sarautu sama da 100 suka kauracewa fadarsu.”

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, sarkin Gaya ya rubuta buƙata zuwa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin a amince da dawo da wasu masu rike da sarautu ciki har da Alhaji Usman Alhaji a matsayin Wazirin Gaya, amma an ƙi amincewa da sunansa da na wasu da dama.

“Abin lura shi ne, ko da Alhaji Usman Alhaji yana matsayin Waziri, akwai hanyoyi da ya kamata a bi kafin a cire shi daga matsayin, kamar tuhuma bisa aikata ba daidai ba, da kuma ba shi damar kare kansa kamar yadda dokokin masarauta suka tanada. Rashin bin waɗannan hanyoyi abin Allah wadai ne kuma rashin adalci ne.

“Ba mu gane dalilin da ya sa sarkin Gaya ya ware Alhaji Usman Alhaji kawai wajen cire masa sarauta ta Wazirin Gaya ba, alhalin ba shi kaɗai ba ne aka ƙi amincewa da sunansa.”

“Amma muna gode wa Allah, kasancewar Alhaji Usman Alhaji ya yi aikin Wazirin Gaya lokacin da masarautar ke da matsayin masarauta mai daraja ta farko na tsawon shekaru uku cikin ƙwazo, kuma tabbas zai ci gaba da kasancewa kuma a kira shi da WAZIRIN GAYA har bayan rasuwarsa.

“A kowane hali, muna jiran hukuncin ƙarshe daga Kotun Koli dangane da wannan lamari, daga dukkan alamu,” a cewar sa.

Leave a Reply