An yi jana’izar mutane 15 da ‘yan bindiga suka kashe a Sakkwato

0
109
An yi jana'izar mutane 15 da 'yan bindiga suka kashe a Sakkwato
Ana yiwa mutane 15 da 'yan bindiga suka kashe Sallar jana'iza

An yi jana’izar mutane 15 da ‘yan bindiga suka kashe a Sakkwato

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Lakurawa ne sun kai wani mummunan hari a kauyen Kwalajiya dake karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto a yammacin ranar Talata, inda suka kashe mutane 15.

Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne a lokacin sallar la’asar, inda suka rika harbin masu ibada da manoma.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe matashi da mahaifinsa a Katsina

Rahotanni sun ce harin ya biyo bayan kashe wasu da ake zargin ‘yan kungiyar ne da aka yi a baya. Maharan sun kuma cinnawa gonaki wuta, sun lalata gidaje, tare da ruguza hanyar sadarwa daya tilo da ke kauyen, lamarin da ya tilastawa mazauna kauyen tserewa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da faruwar harin, inda tace ana cigaba da tantance adadin wadanda suka mutu. Mutane 7 sun jikkata kuma an kai su asibiti.

Mazauna yankin na kira ga gwamnati da ta gaggauta tura karin jami’an tsaro domin hana afkuwar hare-hare, kamar yadda jaridar Sokoto Facts suka ruwaito.

Leave a Reply