Sinwar tsayayyen ɗan gwagwarmaya ne – Khamene’i

0
39

Sinwar tsayayyen ɗan gwagwarmaya ne – Khamene’i

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba wa marigayi shugaban ƙungiyar Hamas Yahya Sinwar bisa ga gagarumar rawar da ya taka wajen tunkarar ‘yan adawa masu zagon ƙasa, yana mai bayyana shi a matsayin tsayayyen ɗan gwagwarmaya kuma wanda ya sallama komai nasa a gwagwarmaya.

A cikin saƙon da ya aike a ranar Asabar, kwana ɗaya bayan da ƙungiyar Hamas ta tabbatar da shahadar Sinwar, Ayatullah Khamenei ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa, da ‘yan’uwansa, da dukkan waɗanda suka sadaukar da kansu wajen jihadi don neman yardar Allah.

“Ya kasance fitila mai haske da juriya ga dakarun gwagwarmaya. Gwarzo da ya tsaya tsayin daka wajen yaƙar abokan gaba da zalunci,” inji shi.

“Da hikima da jajircewa, ya buge ta (maƙiya) da ƙarfi, inda ya bar ɓarnar da ba za a iya jurewa ba a ranar 7 ga Oktoba a tarihin wannan yanki. Sannan kuma cikin mutunci da alfahari ya hau zuwa samman shahidai”.

Jagoran ya kuma jaddada halin da ake ciki na “gabannin adawa,” yana mai cewa har yanzu ba za a iya dakatar da shi ba duk da shahadar “fitattun mutane.”

KU KUMA KARANTA:Yadda Isra’ila ta kashe shugaban Hamas Yahaya Sinwar

“Wani kamar (Sinwar), wanda ya kwashe tsawon rayuwarsa yana yaƙar maƙiya da azzaluman maƙiya, bai cancanci wata iyaka ba face shahada. Haƙiƙa rashinsa yana da zafi ga ɓangaren tsayin daka, amma wannan fage bai gushe ba yana ci gaba da shahadar manyan mutane irinsu Sheikh Ahmed Yassin, Fat’hi Shaqaqi, [Abdel Aziz] Rantisi, da Ismail Haniyeh, kuma hakan ba zai yi ƙasa a gwiwa ba. ko kaɗan tare da shahadar Sinwar in Allah ya yarda. Hamas tana raye kuma za ta ci gaba da rayuwa,” in ji shi, yayin da yake magana kan shugabannin Hamas da duk Isra’ila ta kashe.

Haka nan kuma ya jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na goyon bayan mayaƙan gwagwarmaya, inda ya ƙara da cewa, “Kamar yadda aka saba, za mu tsaya tsayin daka da mujahidai da mayaƙa masu gaskiya, tare da samun nasara da taimakon Allah.

Hamas ta tabbatar a ranar Juma’a cewa Sinwar ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai a birnin Rafah na Gaza.

Sinwar ya kasance shugaban hukumar siyasa ta Hamas tun lokacin da gwamnatin Isra’ila ta kashe Ismail Haniyeh a watan Yuli.

Leave a Reply