Shugaban ƙasa mafi talauci a duniya ya mutu

0
298
Shugaban ƙasa mafi talauci a duniya ya mutu

Shugaban ƙasa mafi talauci a duniya ya mutu

Daga Shafaatu Dauda Kano

Shugaban ƙasa mafi talauci a duniya, Jose Mujica, na ƙasar Uruguay ya mutu.

Mujica, ya kasance tsohon shugaban ƙasar Uruguay, wanda ya rasu yana da shekaru 89, a duniya.

Mujica ya mulki kasar daga 2010-2015.

Tsohon shugaban ya yi suna kan yadda yake gudanar da rayuwa mai sauki ba tare da burin tara dukiya ba, wanda hakan ya sa ake yi masa lakabi da shugaba mafi talauci a duniya.

KU KUMA KARANTA:Tsohon shugaban ƙasa Umaru ‘Yar’Adua ya cika shekaru 15 da rasuwa

Rahotonni sun bayyana cewa marigayin ya rasu a ranar 13 ga watan Mayu, yana da gida ɗaya a ƙauye tare da ƙaramar mota daya, kuma ya mutu bayan fama da cutar daji.

Leave a Reply