Wata babbar Kotu a Kano ta yi watsi da bukatar Ganduje

0
61
Wata babbar Kotu a Kano ta yi watsi da bukatar Ganduje

Wata babbar Kotu a Kano ta yi watsi da bukatar Ganduje

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Wata babbar kotun jihar Kano ta yi watsi da buƙatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya shigar a gabanta.

Ganduje ya ƙalubalanci hurumin kotun na sauraron ƙarar mai ɗauke da tuhuma 11 da ake yi masa da wasu mutane bakwai.

Tashar Channels tv ta ce mai shari’a Amina Adamu Aliyu, wacce ke jagorantar sauraron karar, ta yanke wannan hukuncin.

Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta ce ƙorafin farko wanda Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma suka gabatar bai da inganci kuma bai cancanta ba.

READ ALSO: Akwai yiyuwar nan gaba kaɗan Ganduje ya dawo jam’iyyar PDP – Sule Lamido

Ta tabbatar da cewa kotun na da ikon sauraron ƙarar, wadda ke ɗauke da zarge-zargen cin hanci, haɗin baki, almundahana da karkatar da kudaden jama’a da yawansu ya kai biliyoyin Naira.

Alƙalin kotun ta jaddada cewa za a ci gaba da shari’ar ko da Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma shida ba su halarta ba,

Haka kuma ta umarci kamfanin Lamash Properties Limited, wanda shi ne na shida a jerin waɗanda ake tuhuma, da ya bayyana a gaban kotu.

Hakazalika ta ɗage zaman kotun kan ƙarar har zuwa ranakun 30 da 31 ga watan Yuli domin cigaba da sauraron shari’ar.

Leave a Reply