Madugun ‘yan adawa a Rasha, Alexei Navalny ya mutu a cewar hukumar da ke kula da gidajen yari a ƙasar Rasha.
Hukumar kula da gidajen yari a Rasha ta faɗa a wata sanarwa cewa Navalny ya kamu da rashin lafiya bayan da ya dawo daga wani ɗan tattaki da ya yi don miƙe ƙafa, inda daga baya ya yanke jiki ya faɗi.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa Navalny ya rasu ne a ranar Juma’a yayin da yake tsare a gidan yari.
Ya mutu yana da shekaru 47.
Navalny wanda ya kasance babban ɗan adawar Shugaba Vladimir Putin ya sha shirya manyan-manyan zanga-zangar adawa da fadar gwamnatin Kremlin.
Ya kuma sha shirya gangamin yaƙi da batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa da abin da ya kan ƙira mulkin kama karya.
Hukumar kula da gidajen yari a Rasha ta faɗa a wata sanarwa cewa Navalny ya kamu da rashin lafiya ne bayan da ya dawo daga wani ɗan tattaki da ya yi don miƙe ƙafa, inda daga baya ya yanke jiki ya faɗi.
Nan take aka ƙira motar ɗaukan marasa lafiya don a duba shi, amma sai rai ya yi halinsa, ta ƙara da cewa.
KU KUMA KARANTA:Bayan ya yi shekaru 37 a Kurkuku, an gano ba shi ne ya yi kisan ba
Mai magana da yawun Navalny, Kira Yarmysh, ta faɗa shafin X cewa tawagar muƙarrabansa ba su samu cikakken bayani kan mutuwarsa ba amma lauyansa ya kama hanyar zuwa garin da ake tsare da shi.
Navalny na tsare ne a gidan yari bayan da aka yanke masa hukuncin shekaru 19 saboda tuhuma da aka masa kan nuna tsattsauran ra’ayi.
A watan Disamba aka mayar da shi wani gidan yari na musamman mai tsauraran matakan tsaro daga wani gidan gyara hali da ke yankin tsakiyar Rasha.