Shugaban sojojin Isra’ila ya amince da shirin kai hari a Rafah

0
172

Shugaban rundunar sojojin ƙasa ta Isra’ila Herzi Halevi ya amince da shirye-shiryen ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa a Rafah da ke kudancin Gaza, a cewar kafofin watsa labaran Isra’ila.

Ya bayyana amincewar tasa ne duk da ƙoƙarin da masu shiga tsakani suke yi na ganin an ƙulla yarjejeniyar tsagaita tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa.

KU KUMA KARANTA: Ɗalibai a faɗin Amurka na ci gaba da yin zanga-zangar nuna adawa da yaƙin Isra’ila a Gaza

An amince da shirye-shiryen ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa a Rafah ne yayin ganawar da aka yi tsakanin Halevi, da kwamadan soji na kudacin Isra’ila Yaron Finkelman da sauran manyan kwamandojin rundunonin tsaron Isra’ila, a cewar jaridar The Jerusalem Post.

Hakan na faruwa ne bayan Ministan Tsaron Isra’ila mai tsattsauran Bezalel Smotrich ya yi barazanar rusa gwamnatin Firaiminista Benjamin Netanyahu idan ya amince da tayin Masar na tsagaita wuta a Gaza.

Leave a Reply