Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin sabuwar hukumar gudanarwa da hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) ya kuma miƙawa majalisar dattawan Najeriya domin tabbatar da hakan.
Shugaban a cikin ƙudurinsa na tabbatar da gudanar da aikin Hajji na shekarar 2024 ba tare da matsala ba, ya naɗa waɗannan mutane a Hukumar NAHCON:
Jalal Arabi – a matsayin Shugaba
Aliu Abdulrazaq – Kwamishina, Siyasa, Ma’aikata, & Kuɗi
Prince Anofi Elegushi – Kwamishinan Ayyuka
Farfesa Abubakar A. Yagawal – Kwamishinan Tsare-tsare da Bincike
KU KUMA KARANTA: NAHCON ta ba maniyyata aikin hajjin baɗi mako uku su fara biyan kuɗaɗensu
WAKILAN ZONAL:
Dr. Muhammad Umaru Ndagi — Arewa ta tsakiya
Abba Jato Kala — Arewa maso Gabas
Sheikh Muhammad Bin Othman — Arewa maso Yamma
Tajudeen Oladejo Abefe – Kudu maso Yamma
Aishat Obi Ahmed — Kudu maso Gabas
Zainab Musa – Kudu maso Kudu
Professor Musa Inuwa Fodio — Jama’atul Nasril Islam
Farfesa Adedimizi Mahfouz Adebola — Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci
Shugaban ya umurci waɗanda aka naɗa su sadaukar da kansu wajen ganin cewa ayyukan hukumar alhazai ta ƙasa, kuma su kasance masu inganci da gaskiya da kuma biyan bukatun ‘yan Najeriya.