Shugaban Bangladash na riƙon ƙwarya ya yi ƙiran da a kai zuciya nesa

0
48
Shugaban Bangladash na riƙon ƙwarya ya yi ƙiran da a kai zuciya nesa

Shugaban Bangladash na riƙon ƙwarya ya yi ƙiran da a kai zuciya nesa

Yunus mai shekaru 84, da ya taɓa lashe kyautar Nobel, ya dawo daga Turai a wannan makon don jagorantar gwamnatin wucin gadi, da ke fuskantar babban ƙalubale na kawo ƙarshen rikice-rikice da aiwatar da sauye-sauyen dimokuraɗiyya.

A jiya Asabar shugaban riƙon ƙwarya na Bangladesh Muhammad Yunus ya yi ƙira ga samun haɗin kan addinai bayan ganawa da mahaifiyar ɗalibar da ‘yansanda suka harbe har Lahira, lamarin da ya janyo zanga-zangar da ta kawo ƙarshen mulkin Sheikh Hasina na tsawon shekaru 15.

Yunus mai shekaru 84, da ya taba lashe lashe kyautar Nobel, ya dawo daga Turai a wannan makon don jagorantar gwamnatin wucin gadi, da ke fuskantar babban kalubale na kawo karshen rikice-rikice da aiwatar da sauye-sauyen demokradiyya.

Ya shaida wa manema labarai cewa “Hakinmu shi ne gina sabuwar Bangladesh,”

Hare-haren ramuwar gayya da aka kai kan mabiya addinin Hindu tsiraru a kasar tun bayan hambarar da gwamnatin Hasina, ya haifar da fargaba a makwabciyar kasar Indiya da kuma fargaba a cikin gida.

A yayin wata ziyara da ya kai birnin Rangpur da ke arewacin kasar, Yunus ya yi kira da a kwantar da hankali, ta hanyar tunawa da karrama Abu Sayeed, dalibi na farko da aka kashe a rikicin na watan jiya.

KU KUMA KARANTA:Firaministar Bangladesh, Sheikh Hasina, ta sauƙa daga mulki

Ya kara da cewa “Abu Sayeed yanzu yana cikin kowane gida, yadda ya tsaya muma haka muke yi”. “Babu bambance-bambance a Bangladesh ta Abu Sayeed.”

A ranar 16 ga watan Yuli ne ‘yan sanda suka harbe Sayeed, mai shekaru 25, sa’adda ‘yan sanda suka fara kai farmaki kan masu zanga-zangar da dalibai suka jagoranta ta kin jinin gwamnatin Hasina.

Hasina, mai shekaru 76, ta fice daga kasar da jirgin sama mai saukar mai saukar ungulu zuwa makwabciyar kasar Indiya a ranar Litinin, yayin da masu zanga-zangar suka mamaye titunan Dhaka a wani gagarumin yunkurin kai karshen mulkinta.

Ana zargin gwamnatinta da cin zarafin bil adama da suka hada da kisan gillar da aka yi wa dubban abokan hamayyarta na siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here