Shugaban al’ummar Falasɗinawa a Najeriya ya ziyarci ofishin Neptune Prime, ya yi kira da a kawo ƙarshen kisan ƙare dangi a Gaza

0
352
Shugaban al'ummar Falasɗinawa a Najeriya ya ziyarci ofishin Neptune Prime, ya yi kira da a kawo ƙarshen kisan ƙare dangi a Gaza
Shugaban kamfanin jaridar Neptune Prime Dakta Hassan Gimba tare da Shugaban al'ummar Falasɗinu a Najeriya Ibrahim Ramzy

Shugaban al’ummar Falasɗinawa a Najeriya ya ziyarci ofishin Neptune Prime, ya yi kira da a kawo ƙarshen kisan ƙare dangi a Gaza

Shugaban al’ummar Falasɗinawa a Najeriya, kuma mai sharhi kan yankin Gabas ta Tsakiya, Abu Ibrahim Ramzy, tare da rakiyar wani mai fafutukar ‘yancin Falasɗinu, Abu Safiah Jabeer, sun kai ziyara ta musamman a hedikwatar ofishin Neptune Prime a ranar Litinin, a Abuja.

Ziyarar dai an yi ta ne da nufin nuna godiya ga ƙungiyar kafafen yaɗa labaran da ke ba da goyon baya ga al’ummar Falasɗinu.

Ramzy ya yaba wa Neptune Prime saboda sadaukarwar da ta yi na “yaɗa kisan kiyashin da ake yiwa Falasɗinawa” da kuma tsarin “ɗan’Adam a farko.” Wato ran ɗan’adam ya fi komai daraja.

Ramzy ya jaddada cewa “Falasɗinawa sun cancanci ‘yanci” kuma ya yi kira ga goyon bayan duniya.

Ya kuma ba da damar zama tushen duk wata tambaya game da wahalhalun da ke faruwa a Falasɗinu da Gaza.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 7 tare da raunata wasu da dama

A nasa jawabin, Babban Daraktan Neptune Prime, Dakta Hassan Gimba, anipr, ya gode wa baƙin da wannan ziyara da suka kawo masa. Sannan ya sake jaddada sadaukarwar gidan jaridar Neptune Prime kan yin adalci. Dakta Gimba ya jaddada cewa nuna goyon bayansa babu bambancin ƙabila da addini, domin kowane ɗan’Adam ya cancanci a yi masa adalci.

An kammala tattaunawar ne da kiran ɗaukar mataki daga Abu Ibrahim Ramzy, wanda ya buƙaci Najeriya da ɗaukacin ƙasashen Afirka da su “ɗauki mataki na gaba” domin nuna goyon baya ga al’ummar Falasɗinu.

Leave a Reply