Sheikh Ibrahim Makari, Limamin Masallacin Abuja, ya karɓi baƙuncin baƙin Balarabe

2
324

Shararran malamin addinin musulunci a Najeriya, kuma babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maƙari ya karɓi bakuncin Ibrahim Hamisu, wanda akafi Sani da baƙin balarabe a gidan shi dake Abuja.

A cikin satin nan ne dai idan baku manta ba Neptune Hausa ta kawo muku labarin Baƙin Balarabe daya ɗauko hanya daga Katsina a raƙumi, da niyyar zuwa Abuja domin yi ma Farfesa Ibrahim Makari barka da Shan-ruwa.

Daga bisani, mun samu labari cewa Farfesan ya dakatar dashi cewa ya hawo mota, duba da matsalolin rashin tsaro da ake fama dasu a Najeriya.

A rahoton da muka samu dai, Baƙin Balarabe ya samu ƙyakkawar tarba daga Sheikh Ibrahim Makari, inda ya bashi masauki tare da yi mashi rakiya zuwa babbar majalissar ƙasa.

2 COMMENTS

Leave a Reply