Sheikh Ibrahim Makari, Limamin Masallacin Abuja, ya karɓi baƙuncin baƙin Balarabe

Shararran malamin addinin musulunci a Najeriya, kuma babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maƙari ya karɓi bakuncin Ibrahim Hamisu, wanda akafi Sani da baƙin balarabe a gidan shi dake Abuja.

A cikin satin nan ne dai idan baku manta ba Neptune Hausa ta kawo muku labarin Baƙin Balarabe daya ɗauko hanya daga Katsina a raƙumi, da niyyar zuwa Abuja domin yi ma Farfesa Ibrahim Makari barka da Shan-ruwa.

Daga bisani, mun samu labari cewa Farfesan ya dakatar dashi cewa ya hawo mota, duba da matsalolin rashin tsaro da ake fama dasu a Najeriya.

A rahoton da muka samu dai, Baƙin Balarabe ya samu ƙyakkawar tarba daga Sheikh Ibrahim Makari, inda ya bashi masauki tare da yi mashi rakiya zuwa babbar majalissar ƙasa.


Comments

2 responses to “Sheikh Ibrahim Makari, Limamin Masallacin Abuja, ya karɓi baƙuncin baƙin Balarabe”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Sheikh Ibrahim Makari, Limamin Masallacin Abuja, ya karɓi baƙuncin baƙin Balarabe […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Sheikh Ibrahim Makari, Limamin Masallacin Abuja, ya karɓi baƙuncin baƙin Balarabe […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *