Shehu Sani ya caccaki El-Rufai saboda ya bar bashi mai yawa a jihar Kaduna

0
438

Tsohon ɗan majalisar wakilai, Shehu Sani, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, bisa zargin barin jihar da bashi mai yawa, yayin da ya yi iƙirarin cewa bai taɓa sata a asusunta ba.

Sani ya ƙalubalanci El-Rufai da ya bayyana kadarorin sa ta hanyar buga abin da ya ƙunsa a fom ɗin da ya miƙa a ofishin ‘Code of Conduct Bureau’.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, Sani ya caccaki tsohon gwamnan, yana mai cewa yanzu ya dawo kan ‘shafinsa na Twitter’.

Mai sukar al’ummar ya yi iƙirarin cewa El-Rufai na jiran a ba shi muƙami ne daga wurin shugaban ƙasa Bola Tinubu, bayan kowa yasan shi kuma ya goyi bayan Rotimi Amaechi ne, a shi ya yiwa aiki a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.

Ya rubuta cewa, “El-rufai, Gwamna mai ritaya yanzu ya koma ‘blog a Twitter’ a lokacin da yake jiran muƙami daga wajen Tinubu, bayan ya yi aiki da Amaechi kuma ya watsar da labarai marasa kyau kuma ya yi munanan kalamai game da Tinubu.

KU KUMA KARANTA: Tsohon Gwamna El-Rufai ya zargi Buhari da sakaci wajen yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga a Najeriya

“Kun bar wa ‘ya’yanmu da jikokinmu da ke Jihar Kaduna babban bashin da za su biya, kuma kun yi iƙirarin cewa ba ku taɓa sata a asusun Jihar Kaduna ba.

“Ɗaya daga cikin ‘yan barandan naku ma ya yi iƙirarin cewa kun fi talauci a yanzu.

Na jajirce ku bayyana kadarorinku a bainar jama’a ta hanyar buga abin da ke cikin fom ɗin da kuka gabatar a Ofishin Code of Conduct Bureau, na 2015 da na 2023.

Leave a Reply