Sharaɗin zaman lafiya a wurinmu shi ne a daina yaƙar Falasɗinawa – Nasrallah

0
97
Sharaɗin zaman lafiya a wurinmu shi ne a daina yaƙar Falasɗinawa - Nasrallah

Sharaɗin zaman lafiya a wurinmu shi ne a daina yaƙar Falasɗinawa – Nasrallah

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban ƙungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah ya yi wa al’ummar Lebanon jawabi dangane da harin da aka kai na na’urar sadarwa ta Hezbollah har karo biyu abin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 32 sannan fiye da 3,000 suka jikkata.

A daidai lokacin da shugaban na Hezbollah ke jawabi, jiragen yaƙi na Isra’ila na shawagi ƙasa-ƙasa a kan masu kallon jawabin na shugaban ƙungiyar.

A jawabin nasa, Hassan Nasrallah ya ce burin Isra’ila shi ne jefa tsoro a zukatan mutane, inda ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya.

KU KUMA KARANTA:Kotun Duniya ta ayyana mamayar da Isra’ila ke yi wa Falasɗinu a matsayin haramtacciya

“Idan dai har ba su daina hare-hare a kan Falasɗinawa ba to ba za mu bar kudancin Isra’ila ba. Ya kamata su sani cewa su wawaye ne. E gaskiya ne suna da fasahar zamani amma sun kasa fahimtar cewa mun muna taƙama da imanin da yake ƙara mana ɗamara.”

Hassan Nasarallah ya ƙara da cewa “ana ta maganar yaƙi ko cimma yarjejeniya. Muna sanar da duniya cewa a wurinmu zaman lafiya kawai shi ne a daina yaƙar Falasɗinawa sannan Isra’ila ta fice daga yankunan Falasɗinawa da ta mamaye.”

Leave a Reply