Shanyewar ɓarin jiki, ba ƙarshen rayuwa ba ne: Labarina bayan shanyewar ɓarin jiki

0
378

Daga Ibraheem El-Tafseer

Physiotheraphy Hausa, ta kawo labarin wani magidanci wanda ya haɗu da larurar shanyewar ɓarin jiki, labarin abin tausayi ne matuƙa. Ga yadda labarin ya fara; “A ranar da na sami wannan larura, na tuƙo motata tun daga Abuja har zuwa Kano cikin walwala da ƙoshin lafiya. Babu wata alama ta rashin lafiya da nake ji a jikina a lokacin. Amma sauƙata ke da wuya zan shiga gidana sai na ji wani matsanancin ciwon kai da hajijiya sun ɗauke ni, kafin ƙiftawar ido sai na yanke jiki na faɗi. Sai na yi amai, kuma ɓangarena na dama ya yi nauyi sosai har ba na iya ɗaga hannuna da ƙafata.

Amma cikin ikon Allah ina cikin hayyaci na, ina gane duk wanda ya zo kaina. Bayan maƙwabcina ya ji ƙaƙarin aman da na yi, sai ya rugo da gudu domin kawo min ɗauki.

Aka garzaya da ni asibiti, likita ya ce jinina ne ya hau, kuma har na sami shanyewar ɓarin jiki, ɓarina na dama ya shanye.

Abin mamaki shi ne bayan ba na iya motsa ɓarina na dama, idan an taɓa ni kuma ba na ji. Abin takaicin ma shi ne ana magana ina ji, kuma ina ganewa, amma ni ba na iya maganar. Idan ma aka tambaye ni zan gane tambayar amma bayar da amsa sai ta gagara, sai dai kawai na fashe da kuka don takaici.

Bayan an ba ni taimakon gaggawa sai aka ce za a kwantar da ni domin ina buƙatar kulawa sosai.

Bayan kwanaki biyar, muryata ta ɗan fara fitowa amma duk da haka tana sarƙewa, ba kowa ne yake ganewa ba. Sai likita ya ce jikina ya yi kyau don haka zai sallame ni. Amma zan dawo na dinga ganin likitan zuciya duk bayan sati biyu, sannan zan je ɓangaren “gashi”.

A lokacin da aka ce “gashi” a gaskiya na tsorata sosai saboda a tunanina zuwa za ai a riƙa saka ni cikin wani inji da yake gasa mutane da wuta.

KU KUMA KARANTA: Amfanin yalo da muhimmancinsa ga lafiyar jikin ɗan adam

Sai da na je likitocin ɓangaren suka yi min bayani cewa ai ni ba na buƙatar “gashi”. Saboda haka, suka ce na kwantar da hankalina za a ci gaba da kula da ni har aikin ɓarin jikina ya dawo.

Haka abin yake kuwa, domin har kawo yanzu da na fara dogarawa da sanda har nake iya tafiya ba a taɓa sakamin wani abu mai zafi ko wuta a jiki na ba. Sai daga baya aka yi min bayani cewa ai likitocin fisiyo ake ce musu.

Godiya ga likitocin fisiyo domin tun ba na iya zama suke ɗawainiya da ni zuwa yanzu ga ni ina iya dogarawa da sanda na yi tafiya. Kuma sun tabbatar min cewa nan ba da daɗewa ba za su yayeni daga dogarawa da sandan ma, sannan na dawo tafiya ni kaɗai kamar yadda nake yi kafin larurar.

Hmmm! wato in taƙaice muku zance dai, idan mutum ya sami wannan larura, yana dawowa tamkar jariri ne. Domin a wancan lokacin fa ba na iya riƙe fitsari ko bayan-gida, kuma ba na sanin na yi. Ba na iya cin abinci da hannuna na dama, idan ma matata ta sakamin abinci a baki to bakin ba zai rufu ba, sai abincin ya zirare ya zubo domin bakin ya karkace.

Hakan nan, ba zan iya magana domin ai min wani abu da nake buƙata ba. Sai dai a kwantar a tayar da ni, sannan a jujjuyani hagu zuwa dama kamar yadda likitan fisiyo ya ce.

Kai jama’a! Wato wannan larura ko maƙiyinka ba za ka so ta same shi ba. Amma na san wanda ya taɓa samun wannan larura ne kaɗai zai gane abin da nake nufi sosai.

Allah ya ƙara mana lafiya.

Leave a Reply