Sarkin Musulmi a Najeriya ya ayyana gobe Litinin a matsayin ranar 1 ga Rabi’ul Awwal

0
175
Sarkin Musulmi a Najeriya ya ayyana gobe Litinin a matsayin ranar 1 ga Rabi'ul Awwal
Sultan Muhammad Saad Abubakar III

Sarkin Musulmi a Najeriya ya ayyana gobe Litinin a matsayin ranar 1 ga Rabi’ul Awwal

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana ranar Litinin 25 ga watan Agusta, 2025, a matsayin ranar farko ta Rabi’ul Awwal 1447AH.

Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sakkwato.

KU KUMA KARANTA: A fara duban watan Shawwal ranar Asabar – Sarkin Musulmi

Ya ce, sanarwar ta biyo bayan rahoton kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi tare da kwamitin ganin wata na ƙasa, wanda ya tabbatar da cewa ba a samu ganin jinjirin wata ba daga kwamitocin ganin wata a faɗin ƙasar nan, a ranar Asabar 23 ga watan Agusta, 2025, daidai da 29 ga watan Safar 1447AH.

Ya bayyana cewa ranar Lahadi 24 ga Agusta, 2025, ita ce ranar 30 ga watan Safar, don haka ne ranar Litinin ta zama 1 ga Rabi’ul Awwal 1447AH.

Leave a Reply