Sarkin Kano Sanusi ya yi Hawan sallah babba duk da jami’an tsaron da suka zagaye gidansa domin hana hawan

0
153
Sarkin Kano Sanusi ya yi Hawan sallah babba duk da jami'an tsaron da suka zagaye gidansa domin hana hawan

Sarkin Kano Sanusi ya yi Hawan sallah babba duk da jami’an tsaron da suka zagaye gidansa domin hana hawan

Daga Jameel Lawan Yakasai

Duk da cewar rundunar ‘Yan Sanda Kano sun umarci sarakuna biyu da cewar kada wanda yayi Hawan bikin babbar sallah a wannan rana bisa al’adar masarautar Kano na aiwatar da hawan daushe wanda shi ake kashegarin sallah,

Sai dai Karamar sallah data wuce bayan umarnin dakatar da hawan sallah, Sarkin Kano na 16 Malam Sanusi Lamido Sanusi ya gabatar da hawan babban daki, wanda ya je ya gaisar da mahaifiyarsa.

Cikin wannan rana kuma an hangi jami’an tsaro sun mamaye gidan sarki Sanusi, da motocin ruwan zafi da tankokin yaki, da sauran motocin tsaro, wanda ake gannin anyi hakan ne domin dakatar da Sarkin wajen gudanar da hawan babban daki,

KU KUMA KARANTA:Sarkin Kano Sanusi, ya bawa ‘yan kasuwar waya da iftila’in gobara ta shafa tallafin Naira miliyan 10

Duk da haka Sarkin ya fito daga cikin gidan sa akan rakumi zuwa fadarsa domin karbar gaisuwa ga hakimai da dakatai da sauran jama’a.

Bayan dawo wa daga karbar gaisuwar kuma aka hangi sarkin ya sake fitowa a cikin mota zuwa kasuwar sayar da wayoyi ya farm center domin gabatar da jaje bisa iftila’in gobara da sukayi.

Bayan ya koma gida, Sarkin ya yi sabon shiri ya fita ta kofar fatalwa a mota domin gabatar da hawan babban daki a cikin mota, tare da rakiyar jama’a, kuma ya dawo ta kofar kudu duka dai agaban jami’an tsaro

Leave a Reply