Sarakunan yarbawa sun buƙaci Tinubu ya ba su muƙamai a mulkin shi

0
367

Wata kungiyar sarakunan gargajiya a yankin kudu maso yamma da ‘yankin yarbawa na shiyyar arewa ta tsakiya, ƙarƙashin inuwar ƙungiyar yarbawa ta Obas, ta buƙaci zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya ba wa sarakunan ƙungiyar aiki a ƙundin tsarin mulki.

Sarakunan sun yi wannan buƙata ne a saƙonsu na taya Tinubu murnar nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata.

Shugaban ƙungiyar, Elerinmo na Erinmo, Oba Michael Ajayi, Molokun na Atijere, Oba Samuel Adeoye, wanda shi ne shugaban inuwar gamayyar ƙungiyar kuma tare da babban sakataren ƙungiyar, Olukotun na Ikotun-Ile ne suka sanya hannu kan saƙon , Oba Abdulrasaq Abioye.

KU KUMA KARANTA: Sarakunan Yarbawa sun bayyana goyon bayansu ga Tinubu

Sarakunan sun kuma buƙaci zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da ya zama babban nasara ta hanyar kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa, tare da yin kira ga sauran ‘yan takarar shugaban ƙasa da suka sha kaye a zaɓe, da su marawa Tinubu baya domin ci gaban ƙasar nan cikin gaggawa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna ƙira ga waɗanda suka faɗi zaɓe da su amince da sakamakon da aka samu, su ajiye duk wani bambance-bambance a gefe, su haɗa kai da waɗanda suka yi nasara domin amfanin ƙasa baki daya.

“Muna yaba wa Shugaba Buhari, Shugaban hukumar INEC, (Prof. Mahmoud Yakubu) bisa jajircewar da suka yi wajen ganin an gudanar da ingantaccen zaɓe.

Dimokuraɗiyya tafiya ce ba manufa ba.

“Mu kuma sarakunan Yarbawa muna so mu yi kira ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da ya yi la’akari da bai wa sarakunan gargajiya ayyukan da kundin tsarin mulki ya tanada a ƙasar wanda muke ganin zai taimaka matuka wajen kawo ribar dimokuraɗiyya a kusa da yankunan karkara da kuma daƙile rashin tsaro a ƙasar nan a matsayinmu na manyan jami’an tsaro na sassanmu daban-daban.” In ji sanarwar.

Leave a Reply