Sanata Ibrahim Bomai ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai 50 a ƙasar Indiya, ‘yan asalin jihar Yobe

0
263
Sanata Ibrahim Bomai ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai 50 a ƙasar Indiya, 'yan asalin jihar Yobe
Ɗaliban tare da Sanata Ibrahim Bomai a filin jirgin sama na Abuja

Sanata Ibrahim Bomai ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai 50 a ƙasar Indiya, ‘yan asalin jihar Yobe

Ɗalibai 50 daga yankin Sanatan Yobe ta Kudu sun tashi zuwa ƙasar Indiya domin ci gaba da karatu a ƙarƙashin shirin tallafin karatu na Sanata Ibrahim Mohammed Bomai. Ɗaliban, waɗanda aka zaɓo daga ƙananan hukumomi huɗu na jihar, za su karanci fannoni kamar Artificial Intelligence, Data Science, da Cyber ​​Security.

Sanata Bomai ya taya waɗanda suka ci gajiyar tallafin karatun murna, inda ya buƙace su da su kasance jakadun jihar Yobe da Najeriya. Ya jaddada cewa tallafin na daga cikin ƙudirinsa na ƙarfafa matasa ta hanyar ingantaccen ilimi.

KU KUMA KARANTA: Sanata Ibrahim Bomai ya ƙaddamar da shirin bayar da tallafin karatu don inganta ilimi a Yobe ta Kudu (Hotuna)

A baya gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yabawa Sanata Bomai bisa wannan shiri, inda ya bayyana shi a matsayin wani ƙoƙari na ɗaukaka darajar rayuwar ‘yan ƙasa. Ana sa ran shirin bayar da tallafin zai ƙarawa waɗanda suka ci gajiyar ƙarfin gwiwa da kuma ƙarawa jihar Yobe martabar zuba jari a fannin ilimi da ƙirƙire-ƙirƙire.

Leave a Reply