Sama da mutane 70 ne suka mutu, sakamakon rugujewar mahaƙar Zinari a ƙasar Mali

0
127

Daga Maryam Umar Abdullahi

Wata ma’adina da ake haƙar zinari ta bayan fage ta ruguje a ƙarshen makon da ya gabata a ƙasar Mali, inda ta kashe mutane sama da 70. Kamar yadda wani jami’i ya faɗa a jiya Laraba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike bisa fargabar cewa adadin na iya karuwa.

Wani babban jami’i a hukumar kula da ma’adinan ƙarƙashin ƙasa da aikin haƙar mu’adinai (National Geology and Mining Directorate) ta tabbatar da cikakkun bayanai ga Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press kuma ya ƙira lamarin da haɗari mai muni.

Akwai kusan mutane 100 a cikin mahaƙar ma’adinan a lokacin rugujewar, a cewar Abdoulaye Pona, shugaban hukumar kula da ma’adinan ƙasar Mali, wanda ya je wurin.

KU KUMA KARANTA: Falasɗinawa na cin abincin dabbobi saboda yadda yaƙin Isra’ila ya jawo yunwa a Gaza

Ana gudanar da bincike kan musabbabin rugujewar da ta faru a gundumar Kangaba da ke kudu maso yammacin yankin Koulikoro a ranar Juma’a. An fara ba da rahoto a ranar Talata a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ma’adinai ta fitar da ta ƙiyasta cewa “da yawa” masu haƙar ma’adinai sun mutu.

Irin waɗannan bala’o’i sun zama ruwan dare a ƙasar Mali, wadda ita ce ƙasa ta uku da ke samar da zinari a Afirka. Masu aikin haƙar ƙananan ma’adinai na yau da kullum ana zarginsu. Ana zargin masu aikin haƙar ƙananan ma’adinai na yau da kullum da yin watsi da matakan tsaro, musamman a wurare masu nisa.

Bethe yace, “Dole ne jihar ta samar da tsari ga wannan fannin na haƙar ma’adinai don guje wa irin waɗannan haɗarurruka a nan gaba,” in ji Berthé.

Sanarwar ma’aikatar ma’adinai ta “yi matuƙar nadamar” rugujewar, kuma ta buƙaci masu haƙar ma’adinai da al’ummomin da ke zaune kusa da wuraren haƙar ma’adinai su “kiyaye ƙa’idojin kariya.”

Leave a Reply