Sake zaɓen Fintiri, nasara ce ga demokraɗiyya – PDP

2
637

Jam’iyyar PDP ta bayyana nasarar da Gwamna Ahmadu Fintiri ya samu a zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa a matsayin wani gagarumin nasara ga dimokuraɗiyya da kuma barin jama’a su zaɓi a’ayinsu.

Jam’iyyar a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar a Abuja ranar Talata, ta kuma bayyana sake zaɓen Fintiri a matsayin nasara a kan azzalumai da ‘yan ta’adda da ke neman ƙwace iko da jihar ba bisa ƙa’ida ba.

KU KUMA KARANTA: INEC ta bayyana Gwamna Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Adamawa

Ya ce farin cikin da ‘yan ƙasa ke yi ba tare da ɓata lokaci ba a jihar da ma faɗin ƙasar nan a sanarwar da Fintiri ya yi a hukumance a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaɓe ba tare da la’akari da munanan tsare-tsare ba, hakan ya tabbatar da cewa jam’iyyar PDP da ɗan takararta sun kasance zaɓin jama’a.

“Nasarar da Fintiri ta samu ya tabbatar da cewa ba za a iya murƙushe son zuciyar mutane ba ko da kuwa makircin azzalumai, masu mulki da masu ƙwacen mulki.

“Makircin wasu ‘yan ƙalilan waɗanda, da tsananin kishi, suka nemi murguɗa mulkin dimokaraɗiyyar mu, da murƙushe harkokin zaɓe, da yin sulhu a ɓangaren shari’a, da murƙushe jama’a da kuma kafa tsarin mulkin da bai da ce ba a harkokin siyasa.”

Mista Ologunagba ya jinjinawa jajircewa da al’ummar jihar suka nuna wajen bijirewa yunƙurin da kwamishinan zaɓe na INEC Hudu Ari da sauran su ke yi na kawo ruɗani a jihar.

“Jam’iyyar mu ta kuma yaba wa jami’in kula da masu kaɗa ƙuri’a na jihar Adamawa, Mohammed Mele bisa jajircewarsa wajen tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da adalci, bin doka da oda da dimokuraɗiyya wajen gudanar da aikinsa.”

Ya kuma jinjinawa irin rawar da masu sa ido kan zaɓukan ƙasa da ƙasa da na cikin gida da kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin farar hula da sauran masu kishin Najeriya suka taka wajen tabbatar da cewa an baiwa jam’iyyar PDP da Alhaji Fintiri wa’adin mulkin da ‘yan ƙasa suka yi cikin ’yanci ba tare da masu maye gurbinsa ba.

Ya taya Fintiri da al’ummar jihar Adamawa murna, ya kuma buƙaci gwamnan da ya ci gaba da gudanar da ayyukansa na kawo sauyi ga al’umma bisa tsarin dimokuraɗiyya da tsare-tsare da manufofin jam’iyyar PDP.

2 COMMENTS

Leave a Reply