Saboda talauci, wata mata ta sayar da jikanta ɗan wata uku

0
231

Wata mata ta sayar da jikanta mai watanni uku a duniya a kan kuɗi Naira 50,000 a jihar Anambara da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Wacce ake zargin Oluchukwu Nwosu ta sayar da jaririn ne ba tare da sanar da ɗiyarta Ijeoma ba, wacce ta haifi yaron ba tare da aure ba, cewar rahoton Premium Times.

Chidinma Ikeanyionwu, hadimar kwamishiniyar mata da walwalar jama’a a jihar, Ify Obinabo, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba.

Ikeanyionwu ta ce a yanzu kwamishinan ta ceto yaron, sannan ta kuma taimaka wajen sanya ‘yan sanda cafke wacce ake zargin.

Wacce ake zargin, Misis Nwosu, da take magana bayan ta shiga hannu, ta yi iƙirarin cewa halin talauci da ƙasa kula da jaririn ne ya tilasta mata sayar da shi.

KU KUMA KARANTA: Yara miliyan 2.2 a Jamus na cikin haɗarin talauci

Matar ta ce wannan shi ne karo na uku da ɗiyarta ta haihu ba tare da aure ba, inda ta yi nuni da cewa akwai wasu yara biyu dukkaninsu maza, ana kula da su a wani gidan marayu da ke birnin Awka.

Ta ce tun daga lokacin da ɗiyarta ta haifi yaron da ƙyar suke samun abin da za su ci, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Ta yi iƙirarin cewa wani mutum mai suna Tochukwu Asiegbu ya tuntuɓe ta inda ya amince ya sayi yaron a kan farashin Naira 50,000.

A nasa ɓangaren, Mista Asiegbu, wanda aka ruwaito ya sake sayar da yaron, ya ce ya samu ribar Naira 30,000 ne kawai daga sayan jaririn.

Sai dai Evelyn Egwuatu, wacce aka ɗauko jaririn daga hannunta, ta ce ta biya wata mata Ebelechukwu Uba kudi Naira 200,000 domin ta sayo yaron.

Leave a Reply