Ruwan sama mai ƙarfi ya kashe mutane 41 a Koriya ta Kudu, ana ci gaba da neman wasu

2
398

Daga Nusaiba Hussaini

Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutane tara da har yanzu ba a gansu ba sakamakon zaftarewar ƙasa da wasu al’amura da suka faru sakamakon mamakon ruwan sama da aka shafe mako guda ana yi a Koriya ta Kudu.

Ambaliyar ruwa da ta aukawa Koriya ta Kudu tun ranar 9 ga watan Yuli ya yi sanadin mutuwar mutane 41, tara kuma ba a ganta ba, wasu 35 kuma suka jikkata.

Hakazalika ruwan sama ya tilastawa kimanin mutane 12,780 yin hijira tare da barin gidaje kusan 28,600 ba su da wutar lantarki.

KU KUMA KARANTA: Ruwan sama ya kashe mutane 7, ya raunata da dama a Delta

A yayin wani taron Majalisar Zartarwa a ranar Talata, Shugaba Yoon Suk Yeol ya umarci jami’ai da su tattara dukkan albarkatun da ake da su don ƙubutar da duk wani mai yuwuwar tsira, taimakawa waɗanda abin ya shafa da kuma gudanar da ayyukan farfaɗowa
kuma gudanar da ayyukan farfaɗowa.

Yoon ya ce gwamnati na shirin ayyana manyan wuraren da ruwan sama ya shafa a matsayin yankunan bala’o’i na musamman don taimakawa wajen gaggauta farfaɗowa.

Ma’aikatar tsaro daban ta ce tana aikewa da kayan aiki da sojoji 11,000 a ranar Talata don tallafawa ƙoƙarin gwamnati na gano mutanen da suka ɓata da kuma maido da ɓarnar da aka yi.

An ba da rahoton yawancin ɓarnar da aka yi a yankunan tsakiya da kudancin Koriya ta Kudu, tare da ɓacewar mutane tara da aka jera a lardin Gyeognsang da ke kudu maso gabashin ƙasar ko kuma birnin Busan na kudu maso gabashin ƙasar.

Har ila yau, an bayar da rahoton mutuwar mutane 14 daga wani rami da ke tsakiyar birnin Cheongju, inda motoci 17 ciki har da wata motar safa suka maƙale a wata ambaliyar ruwa da wataƙila ta cika hanyar.

Tun da farko dai hukumomi sun tattara masu ruwa da tsaki da sauran ma’aikata don ceto waɗanda suka tsira da rayukansu da kuma ƙwato gawarwakin kafin a ce sun kawo ƙarshen bincike a cikin ramin a daren ranar Litinin.

Tsananin yanayi kuma yana shafar sauran wurare da yawa a duniya. A farkon wannan watan, ambaliyar ruwa ta mamaye sassan Indiya, Japan, China, Turkiyya da kuma Amurka.

Ko da yake bala’in ambaliya yana faruwa a sassa daban-daban na duniya, masana kimiyyar yanayi sun ce suna da wannan abu guda ɗaya: Tare da sauyin yanayi, guguwa suna tasowa cikin yanayi mai zafi.

2 COMMENTS

Leave a Reply