Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, ya rushe gidaje da dama a Potiskum
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a Potiskum ranar juma’a, ya rushe gidaje da dama a yankuna daban-daban a cikin garin Potiskum.
Ruwan an yi shi ne cikin daren Alhamis wayewar yau juma’a (15th August) inda ya yi mummunan ta’adi, na raba mutane da dama da muhallansu.
Yankunan da abin ya fi shafa sune unguwannin da gidajensu ke kusa da gadar hanyar ruwa. A inda rushewar gidajen ya fi ƙamari sun haɗa da unguwannin Arikime, Ramin Ƙasa, Tandari, Nahuta, Boriya, Rugar Fulani da Unguwar Kuwait.

KU KUMA KARANTA: Za a iya samun ambaliyar ruwa a jihohi 19 a faɗin Najeriya – Gwamnatin tarayya
Sauran unguwannin sune, Old Prison, Filin Nashe, Unguwar Makafi/Majema, Unguwar Jaji bakin kwari, Afghanistan, Tsangaya bakin kwari, Karofi, Bayan Garejin Danjuma da unguwannin bayan Fudiyya Potiskum.
Su waɗannan unguwanni ruwan sama yana musu ambaliya ne sakamakon rashin magudanar ruwa a unguwannin. Kwata-kwata ruwan sama ba ya fita a unguwar, sai dai ya shige gidajen jama’a.

KU KUMA KARANTA: KMT ya ba da tallafin Naira miliyan 1 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Gulani
Zuwa haɗa wannan rahoto babu labarin asarar rayuka, sai dai rushewar gidaje da dama. Neptune Prime ta je inda gini ya faɗa a kan wata mata, amma ita ma ba ta mutu ba.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe (SEMA) ta tura wakilanta don ba da agajin ga waɗanda iftila’in ta shafa.










