Rundunar ‘yansanda ta ba da naira miliyan 50 ga iyalan ‘yansanda da suka mutu a Zamfara

0
218

Daga Idris Umar, Zariya

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Muhammad Shehu Dalijan, a madadin Sufeto Janar na ‘yansandan IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya gabatar da cek ɗin naira miliyan hamsin da dubu ɗari da arba’in da biyar, da naira ɗari da goma sha tara da kobo tamanin da uku (50,145,119.83) ga ’yan’uwa 27 na jami’an ‘yansanda da suka mutu a lokacin da suke bakin aikin su.

Waɗannan cak da aka bayar wani ɓangare ne na shirin IGP a ƙarƙashin tsarin inshorar jin daɗin iyali na ƙungiyar da IGP don taimaka wa iyalan jami’an mu da ke biyan fansho mai tsoka a lokacin da suke raye.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ASP Yazid Abubakar, ya ce CP, ya bayyana haka a takardar ya sa hanu ga manema labarai a Gusau.

KU KUMA KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnoni 16 na goyon bayan kafa ‘yan sandan jihohi

A cewar sa SP Yazid, ya yabawa IGP bisa wannan karamcin da ya nuna, sannan ya kuma yi ƙira ga iyalan jami’an da suka rasu da su yi amfani da kuɗin da kyau da kuma kula da iyalansu.

Malam Yahaya Umar ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin a jawabinsa a madadin sauran waɗanda suka amfana, ya gode wa babban sufeton ‘yansanda da rundunar ‘yansandan jihar bisa wannan tallafi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa za a kashe kuɗaɗen da aka ba su ta hanyar da ta dace.

Yayi fatan samun zaman lafiya a jihar Zamfara da Najeriya baki ɗaya.

Leave a Reply