Rundunar Sojin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar sakin fursunonin yaƙi, da tsagaita wuta na wucin-gadi da Hamas

0
262

Rundunar sojin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar musayar waɗanda aka yi garkuwa da su da kuma tsagaita wuta na wucin-gadi da ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas a Zirin Gaza, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka ruwaito a ranar Talata.

“Rundunar soji na shirin yin amfani da tsagaita wuta domin sake shirya dakarunta a shirye-shiryen faɗaɗa kai hare-haren ta ƙasa zuwa kudancin Gaza,” a cewar kafar yaɗa labarai ta KAN.

A cewar kafar yaɗa labaran, yarjejeniyar da aka cimma ta haɗa da tsagaita wuta na kwanaki huɗu, da kuma sakin wasu ‘yan Isra’ila 50 da Hamas ke garkuwa a musayar Falasɗinawa 150 da ke gidajen yarin Isra’ila.

Isra’ila ta yi ƙiyasin cewa aƙalla Isra’ilawa 239 ne Hamas ke tsare da su bayan harin da aka kai kan iyaka a ranar 7 ga watan Oktoba.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta yi luguden wuta a asitibin Indonesia da ke arewacin Gaza, ta kashe mutane da dama

Isra’ila ta kai hare-hare ta sama da ta ƙasa a Zirin Gaza bayan harin ba-zata na Hamas, inda ta kashe Falasɗinawa sama da 14,128, ciki har da yara 5,840 da mata 3,920, a cewar hukumomin lafiya a yankin.

Dubban gine-gine, da suka haɗa da asibitoci da masallatai da majami’u aka rusa ko lalata a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama da ta ƙasa kan yankin da aka yi wa awanya.

Adadin waɗanda suka mutu a Isra’ila, ya kai kusan 1,200, a cewar alkaluman hukuma.

Leave a Reply