Rumfar rantsar da Abba Gida-gida ta rufta

Rumfar da aka yi don rantsar da sabon gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba kabir Yusuf, ta rufta a daidai lokacin da ake bikin.

Lamarin ya faru a lokacin da sabon gwamnan wanda ake wa lakabi da Abba Gida-gida yake kai tare da matimakinsa da kuma muƙaddashin babban mai shari’a na jihar, wanda ya jagoranci rantsar da sabon gwamnan da mataimakin nasa. Amma dai babu wanda ya ji rauni a cikinsu.

Sabon gwamnan yana shirin barin dandamalin ne bayan rantsar da shi sai kawai rumfar ta rufta inda nan da nan jami’an tsaronsa suka kakkare shi ciki har da kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, Ahmad Gumel.

An katse bikin ta yadda sabon gwamnan bai iya duba faretin masu kayan sarki ba, saboda cincirundon magoya baya da suka yi wa filin wasa na Sani Abacha cikar-kwari ciki da waje.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *