No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kimanin ɗalibai 150 da Gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin karatun digirinsu na biyu sun bar jihar a safiyar yau Juma’a don fara karatunsu a jami’o’in ƙasashen waje daban-daban waɗanda suka haɗa da ƙasar Indiya da Uganda waɗanda kuma ake sa rai za su samu ƙwarewa a fannonin ilimi daban-daban.

Ɗaliban dai su ne rukunin na farko daga cikin ɗalibai 1001 da Gwamnatin ta ɗauki nauyin karatun nasu.

Da yake jawabi game da muhimmancin shirin na tura ɗalibai ƙasashen waje, Gwamn Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa shirin wanda tsohon Gwamnan Kano, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya ƙirƙiro shi ya zama gata ga ’ya’yan jihar don haka gwamnatinsa ta ga dacewar ci gaba da aiwatar da shi.

Gwamnan ya bayyana cewa a bayyane yake a fili yadda waɗanda suka ci moriyar shirin a baya sune ke riƙe da manyan mukamai a cikin gwamnatinsa.

“Wannan aiki da ya yi yana tura ɗalibai ƙasashe waje ya haifar da samun ƙwararru a fannoni daban-daban a jihar daga cikinsu akwai irinsu Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi da Dakta Yusuf Ƙofar Mata da Farfesa Aliyu Isa Aliyu da kuma Mai ba Gwamnan shawara kan ƙirkire-ƙirkire, Bashir Muzakkar da sauransu.

Ana iya tuna cewa, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya gudanar da wannan shirin sau uku a wa’adin mulkinsa na biyu, inda ya tura ɗalibai ƙasashe kusan 16 a faɗin duniya.

A jawabinsa, Kwankwaso ya yaba wa Gwamnatin Jihar bisa ci gaba da ta yi da waɗannan ayyuka na alheri.

Ya yi ƙira ga ɗaliban da su mayar da hankali kan abin da ya kai su don zama masu amfani ga iyayensu da kuma al’ummar jihar da ƙasa gaba ɗaya.

Ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna Babangida Salisu daga ƙaramar Hukumar Tarauni ya yaba wa Gwamnatin Abba wajen yin wannan ƙoƙari na tura su ƙasashen waje inda ya ɗauki alƙawarin yin duk abin da ya kamata don ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...