Real Madrid ta karrama Abderrahim wanda ya rasa iyayensa a girgizar ƙasa a Marocco

0
283
Real Madrid ta karrama Abderrahim wanda ya rasa Iyayen sa a Girgizar Kasa a kasar Marocco Daga Jameel Lawan Yakasai An karrama Abderrahim Ouhida, mai shekara 16 a filin wasa na Santiago Bernabéu, kafin fara wasan Real Madrid da Espanyol a ranar Asabar, a gasar La Liga ta kasar Sifaniya. Abderrahim Ouhida, ya rasa mahaifansa, da yan uwansa mata biyu, da kakansa, bayan faruwar wata girgizar kasa da ta faru a kasar Morocco a watan Satumbar 2023. Tun faruwar lamarin, Madrid ta dauki nauyin kula da shi, har ma ya samu damar kasancewa a karamar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid. A gefe guda kuma, Real Madrid ta dauki nauyin karatunsa domin ganin ya samu rayuwa mai inganci kamar kowa..

Real Madrid ta karrama Abderrahim wanda ya rasa iyayensa a girgizar ƙasa a Marocco

Daga Jameel Lawan Yakasai

An karrama Abderrahim Ouhida, mai shekara 16 a filin wasa na Santiago Bernabéu, kafin fara wasan Real Madrid da Espanyol a ranar Asabar, a gasar La Liga ta kasar Sifaniya.

Abderrahim Ouhida, ya rasa mahaifansa, da yan uwansa mata biyu, da kakansa, bayan faruwar wata girgizar kasa da ta faru a kasar Morocco a watan Satumbar 2023.

KU KUMA KARANTA: Real Madrid ta lashe kofin Laliga a karo 36

Tun faruwar lamarin, Madrid ta dauki nauyin kula da shi, har ma ya samu damar kasancewa a karamar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

A gefe guda kuma, Real Madrid ta dauki nauyin karatunsa domin ganin ya samu rayuwa mai inganci kamar kowa..

Leave a Reply