Rashin tsugunar da ‘yan Boko Haram da suka miƙa wuya babban haɗari ne- Barista Bulama Bukarti

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Masana harkokin tsaro a Najeriya sun ce akwai babban haɗari idan har ‘yan kungiyar Boko Haram din da suka miƙa wuya suka rasa matsugunni.

Masanan sun yi tsokacin ne bayan da hukumomi a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar, suka ce ana fama da ƙarancin wurin ajiye dubban ‘yan ƙungiyar ta Boko Haram da suka miƙa wuya.

Barista Audu Bulama Bukarti, mai sharhi ne kan lamurran tsaro, ya shaida wa BBC cewa akwai hatsarin gaske idan har gwamnati ko hukumomin tsaro suka gaza wajen samar da matsugunnai ga wadannan ‘yan Boko Haram din.

“Babban hatsarin shi ne za su iya kuɓucewa su koma in da suka fito wato ƙungiyarsu, saboda da yawa daga cikinsu yunwa ko rashin yarda da wani abu a kungiyar ne ya sa suke fita daga kungiyar su mika wuya.”

Masanin tsaron ya ce idan har suka je sansanin suka ga babu abincin da za a ci a koshi sannan rayuwa ta ki dadi a wajen, ko kuma duk da sun mika wuya an ki yi musu abin da ya dace misali na rashin mayar da su cikin al’umma, to babban abin da za su fara yi shi ne su gudu su koma kungiyarsu.

Barista Bukarti, ya ce “Abu na biyu za su iya wanke kan wasu waɗanda su ba ‘yan kungiyar ta Boko Haram ba ne sun kuma hadu da su a irin zaman sansani, sai su wanke su don su koma ƙungiyar tasu.”

Ya ce abu na uku tun da ita ƙungiyar Boko Haram din na jin haushin waɗanda suka miƙa wuyan, to za ta iya kitsa hari ta kai irin wuraren da aka ajiye su don ta kashe su.

Masanin tsaron ya ce dole idan gwamnati na son ƙare duk abubuwan da ya lissafa, to na farko shi ne gwamnati ta fito ta faɗa wa mutane gaskiya a kan matsayin mutanen da suka miƙa wuyan.

Ya ce,” Abu na biyu shi ne gwamnati ta yi tsari mai kyau tun da dai za a ci gaba da samun irin waɗannan mutanen da za su rinƙa miƙa wuya.”

Barista Bukarti, ya ce dole sai gwamnati ta smaar da isassun sansanoni na ajiye irin waɗannan mutane da kuma isassun kayan kula da su ciki har da tsare su daga hare-hare, da tabbatar da cewa ba su koma kungiyar ba.

Ƙarin bayani

Kwamandan rundunar yaƙi da matsalar tsaro a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, wadda ake kira ”Operation Haɗin Kai”, Manjo Janar Chris Musa, ya ce ya zuwa yanzu tsofaffin ‘yan ƙungiyar kusan dubu sittin da bakwai (67,000) ne suke jiran a karbe su, sai dai wurin da ake da shi ba zai dauke su ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *