Raɗe-raɗin komawar Jonathan jam’iyar ADC ne ya hana Atiku karɓar katin jam’iyyar

0
277
Raɗe-raɗin komawar Jonathan jam'iyar ADC ne ya hana Atiku karɓar katin jam'iyyar
Atiku Abubakar tare da Goodluck Jonathan

Raɗe-raɗin komawar Jonathan jam’iyar ADC ne ya hana Atiku karɓar katin jam’iyyar

Daga Jameel Lawan Yakasai

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya dakatar da shirin karɓar katin zama ɗan jam’iyar ‘African Democratic Congress (ADC), a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan zai iya shiga takarar shugaban ƙasa a 2027, kuma jam’iyyar ADC ce ke nemansa.

Atiku, wanda a kwanakin baya ya fice daga jam’iyyar PDP bayan da aka daɗe ana taƙaddama a cikin gida, shi ne ya tsara sauya sheƙarsa zuwa ADC.

KU KUMA KARANTA: ADC ba za ta lamunci ƙaƙaba ‘yan takara ko cin amanar jam’iyya ba – David Mark

Jami’an ADC ne za su ba Atiku katin zama mamba a mahaifarsa ta Jada da ke ƙaramar hukumar Jada a jihar Adamawa.

Duk da haka, PUNCH ta tattaro cewa bukin, wanda aka shirya yi a ranar Laraba, 6 ga watan Agusta, an ɗage shi sai baba-ta-gani ba tare da wani bayani a hukumance daga ɓangaren tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba.

Haka zalika, wani jigo a jam’iyar ADC ya shaida wa jaridar PUNCH cewa jam’iyyar ta yi ta tattaunawa da Jonathan kan yiwuwar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Da yake zantawa da jaridar, shugaban jam’iyyar ADC reshen jihar Adamawa, Shehu Yohana, ya ce an dage rajistar da Atiku zai yi a jam’iyyar ba tare da wata sabuwar rana ba.

A halin da ake ciki kuma, wani jigo a jam’iyyar ADC a matakin kasa, wanda baya son a buga sunansa, ya shaida cewa dage karbar katin jam’iyyar ba zai rasa nasaba da rigimar iko ba tsakanin Atiku da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi.

Jigon jam’iyyar ya yi zargin cewa tafiyar siyasa ta Obi ta kwace jam’iyyar ADC a Kudu, lamarin da ya ce ya jefa burin Atikun na zama shugaban kasa cikin barazana.

Leave a Reply