Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana yadda ya kawo hanyar sharewa ahalin Nabeeha hawaye bayan samo wanda zai biya kuɗin fansan da ‘yan bindiga suka nema bayan sace su.
Idan baku manta ba, an ruwaito yadda wasu ‘yan ta’adda suka yi awon gaba da wasu ‘yan gida ɗaya ‘yan mata shida, inda suka nemi kuɗin fansan miliyoyin kuɗaɗe.
Wannan lamari ya ɗauki hankalin ‘yan Najeriya da dama, musamman ganin ya faru ne a babban birnin tarayya Abuja, inda ya fi ko ina tsaro a ƙasar.
Da yake bayyana yunƙurin taimakawa ahalin da suka shiga jimami, babban malamin addinin Islama, tsohon minista kuma mai faɗa a ji a Najeriya, Farfesa Pantami ya samar da mafita.
Ya bayyana cewa, ya magantu da abokinsa da ya amince da biyan aƙalla naira miliyan 50 don tabbatar da an sako waɗannan ahali da ke hannun ‘yan ta’adda.
KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun lakaɗa wa basarake duka har ya suma saboda rashin cika kuɗin fansa
A bayaninsa, ya ce sam ba ya goyon bayan a ba ‘yan ta’adda kuɗaɗen fansa, amma yanayi ya nuna an cutar da ahalin kuma ya kamata a yi hubbasa don taimaka musu.
A jawabinsa da ya yaɗa a kafar Twitter, Pantami ya ce:
“Ni kaina ba na goyon bayan biyan kuɗin fansa ga ‘yan ta’adda. Sai dai kuma tunda ta tabbata jiya mun rasa ‘yarmu Nabeeha, kuma an yiwa sauran yaran 5 barazana kamar yadda na yi magana da mahaifinsu jiya da yau.
“Don haka, na yi magana da wani abokina kuma ɗan’uwa wanda ya amince zai biya sauran naira miliyan 50 na miliyan 60 ɗin nan take.
“Na ba da lambar asusun mahaifin ‘yan matan mai suna, Mansoor Al-Kadriyar, ga abokina kuma ɗan uwa don aikawa da kuɗin kai tsaye. “
Pantami ya ba da shawari da ishara ga mahaifin ‘yan matan da cewa:
“Duk wani ƙarin kuɗin da aka samu ya zuwa jiya, sai uban ya yi amfani da shi wajen yiwa yaran da sauran ‘yan uwa a ahalin jinya da yardar Allah.
“Allah Ta’ala Ya sakawa wannan aboki kuma ɗan uwa da Jannatul Firdaus bisa wannan gudummawar. Ya kuma sakawa duk waɗanda suka bada gudumawa ta kowace hanya da Jannatul Firdaus.
“Ya kuma gafartawa Nabeeha, ya kuɓutar da ‘yan uwanta. Allah kuma ya taimaki jami’an tsaronmu wajen kawo ƙarshen wannan ƙalubale. Allah ya sa Najeriya ta zama wuri mafi alheri garemu baƙi ɗaya.”