No menu items!

Sample Page Title

Date:

Pakistan ta rufe hanyoyin shiga da fita na Islamabad

A ranar Juma’a ƙasar Pakistan ta sanya tsauraran matakan tsaro a cikin da wajen Islambad, don hana magoya bayan tsohon firai minista Imran Khan da aka daure yin maci a babban birnin ƙasar.

Hukumomin ƙasar sun rufe manyan tituna da hanyoyi shiga cikin birnin da kwantenonin jigilar kaya.

Sun dakatar da sabis na wayar salula, rufe makarantu da hada-hadar sufurin jama’a na hukuma.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun kashe sama da mutane 70 a Haiti

Ministan Harkokin cikin gida na Pakistan Mohsin Naqvi ya ce, “babu wanda ya yi farin cikin rufe birnin tare da kwantenonin jigilar kaya, kuma mutane suna fuskantar matsaloli, amma dole ne mutane su fahimci dalili da yasa muke yin haka, kuma saboda wanene, kuma me yasa.”

An jibge jami’an ‘yan sanda da dakaru sa kai a wuraren shiga da fita, kuma gwamnati ta dakatar da taron jama’a na wani dan lokaci a Islamabad.

Haka kuma an sanya irin wadannan matakan tsaro a birnin Rawalpindi da ke makwabtaka da shi, inda hedkwatar sojojin Pakistan ta ke.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...