NNPP ta shirya ƙawance da jam’iyyun adawa

0
228

Jam’iyyar NNPP ta ce a shirye take domin yin haɗaka da kowace jam’iyyar adawa kamar yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya buƙata.

Muƙaddashin shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Abba Kawu Ali, a cikin wata sanarwa ya ce ƙiran da Atiku ya yi abin yabawa ne da kuma maraba.

Sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Talata ta ce irin wannan shiri da aka yi ne ya bai wa jam’iyyun adawa a 2015 damar haɗewa suka kayar da jam’iyyar PDP mai mulki a lokacin.

“Tabbas kofarmu a buɗe take ga haɗin wannan gwiwa ko kawance da duk wani shiri da ɓangarori ko jam’iyyun PDP da LP da APC, muddin haɗin gwiwar ko tsarin zai amfani al’ummar Najeriya da kuma tabbatar da dimokuraɗiyyar ƙasar,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Ba a ba mu kundin hukuncin kotun ɗukaka ƙara ba — NNPP

Ali ya ƙara da cewa a halin yanzu NNPP “tana nazarin yanayin siyasar ƙasar nan,” kuma “za ta yi maraba da kowace jam’iyyar siyasa da duk wani shiri ko tayin tattaunawa da nufin kare al’ummarmu, dimokuraɗiyyance da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a ƙasarmu.”

A makon da ya wuce ne Atiku Abubakar ya nemi haɗin kan jam’iyyun siyasa wajen haɗewa domin yaƙar jam’iyyar APC mai mulki.

Leave a Reply