NNPP ta kori Abdulmumin Jibrin Ƙofa daga jam’iyyar
Daga Jameel Lawan Yakasai
Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano ta kori ɗan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin Kofa, bisa zargin gudanar da ayyukan cin amanar jam’iyya da kuma kasa cika wajibin kuɗin jam’iyya.
Jibrin Kofa wanda ke wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai, yayin wata tattaunawa da gidan jaridar DCL a ranar Juma’a ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne idan ya bar NNPP.
Haka kuma, ya bayyana cewa ya taimaki jam’iyyar mai mulki wajen lashe zaɓe a Kano, kamar yadda ya koma majalisar wakilai a ƙarƙashin jam’iyyar a zaɓen 2023.
Sai dai a taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Asabar, shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Hashim Dungurawa, ya sanar da korar Jibrin, inda ya ce an yanke wannan hukunci ne sakamakon matsanancin suka da yake yi a kafafen yaɗa labarai kan jam’iyya da shugabancinta.
KU KUMA KARANTA: Kawu Sumaila Ya canza sheƙa daga Jam’iyya NNPP Zuwa APC
Dungurawa ya bayyana Jibrin a matsayin “ɗan siyasa mara ƙarfi” wanda nasarar zaɓensa ta samo asali ne daga tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP, ba daga ƙarfin kansa ba.
Shugaban ya ce an kafa kwamiti na sasanci domin tattaunawa da Jibrin bayan hirarsa da tashar talabijin ta Channels , amma fitowar sa ta gaba a kafafen ya tabbatar da cewa ya tsallake iyaka.
“Maimaikon ya zauna a tattaunawa, sai ya ƙara aikata abin da ya sabawa manufar mu, inda ya fito fili ya nuna biyayya ga wani tsari. Shi ya sa muka kore shi. Ba shi da wata gudunmawar da zai bayar,” a cewar sa.









