Kamfanin NNPC zai fara gyaran matatar man fetur ta Kaduna

Gwamnatin Najeriya ta amince ta ƙulla yarjejeniya da wani kamfani a Koriya ta Kudu da zimmar gyara matatar man fetur ta Kaduna da ke arewacin ƙasar.

Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC, Mele Kyari, shi ne ya saka hannu a madadin Najeriya yayin taro kan harkokin lafiya da tawagar ƙasar ke halarta a Koriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Sanarwar da NNPC ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce nan gaba kaɗan za a fara zagayen duba gyaran da za a yi.

A ƙarshen shekarar 2021 ne gwamnatin Najeriya ta ware fiye da dala biliyan ɗaya don gyara matatar mai ta da ke birnin Fatakwal, aikin da ta ce ana ci gaba da yi.

Kazalika, za a ci gaba da irin wannan aiki a matatar ta garin Warri na Jihar Delta.


Comments

One response to “Kamfanin NNPC zai fara gyaran matatar man fetur ta Kaduna”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *