Nijar ta yi wa dubban yara riga-kafin cutar sarƙewar numfashi

0
277

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta rawaito cewa, hukumomin Nijar su shafe tsawon kwanaki huɗu suna gudanar da aikin riga-kafin kamuwa da cutar sarƙewar numfashi ta Diptheria a jihar Zinder da ke zama cibiyar annobar cikin shekaru 20 a ƙasar.

Tun lokacin da cutar ta mashako ta fara ɓarkewa a cikin watan Yuli a Nijar, ta kashe fiye da mutane 200 daga cikin mutane dubu 2 da 936 da suka harbu da ita kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana.

WHO ta ce, a ranar 20 ga watan Nuwamban nan ne, hukumomin kiwon lafiyar Nijar suka ƙaddamar da aikin rigakafin a Matameye da ke  Zinder wadda ke da kashi 48.7 na masu ɗauke da cutar ta Diptheria a ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Mun kusa kawo ƙarshen zazzaɓin cizon sauro a Afirka – UNICEF

Ya zuwa ranar 24 ga wannan wata na Nuwamba, kimanin ƙananan yara dubu 300 ne daga matakin jarirai zuwa ‘yan shekara 14, aka yi wa rigakafin kamuwa da cutar, kuma adadin jami’an kiwon lafiyar da suka gudanar da wannan aikin ya kai dubu 1.

Wannan cuta ta Diptheria dai, na da matukar haɗari kuma tana yaɗuwa ne cikin sauri, inda take haddasa zafin kirji da bushewar maƙoshi, baya ga zazzaɓi da kuma kumburin wuya da ciwon kai da yoyon hanci har ma da tari.

Sai dai rigakafin na zuwa ne a daidai lokacin da Nijar ke shan raɗaɗin takunkuman da aka kakaɓa mata sakamakon juyin mulkin soji na ranar 26 ga watan Yuli, abin da ya haddasa ƙarancin shigowar wasu kayayyaki da suka haɗa da magunguna ciki ƙasar.

Leave a Reply