Ni zan lashe zaɓen 2027 – Sanata Rabi’u Kwankwaso

0
49
Ni zan lashe zaɓen 2027 —Sanata Rabi'u Kwankwaso

Ni zan lashe zaɓen 2027 – Sanata Rabi’u Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce yana da yaƙinin shi zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kwankwaso wanda ya zo na huɗu cikin waɗanda suka yi takarar shugaban ƙasa, ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar a birnin Katsina.

Bayanai sun ce tsohon gwamnan na Jihar Kano ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ƙaddamar da sakatariyar jam’iyyar NNPP, da ke kan titin IBB, a birnin Katsina.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Kwankwaso ya ƙaddamar da sabon ofishin jam’iyyar ne bayan ya je ziyarar ta’aziyyar rasuwar Hajiya Dada, mahafiyar tsohon Shugana ƙasa, Umar Musa Yar’adua wadda ta riga mu gidan gaskiya a makon jiya.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Abba ya ƙaddamar da kwamitocin bincike kan rikicin siyasa da ta’annati da dukiyar Kano

A cewarsa, jam’iyyar da ke kan turbar samun nasara a shirye take ta karɓi ragamar shugabancin ƙasa, jihohi da sauran muƙamai a fadin ƙasar nan zuwa 2027.

“Ina so na tunatar da ku cewa, jam’iyyar PDP ta riga ta mutu, domin muna cikin jam’iyyar, amma tun da ta sauka daga kan tsari, sai muka yanke shawarar raba gari da ita,” inji Kwankwaso.

Kwankwaso ya kuma yi ƙira ga ’yan Najeriya musamman mata da matasa da kada su bari a yaudare su da taliya ko kuɗi a lokacin zaɓe mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here